karin Haraji: Mahautan Suleja sun yi hijira zuwa Abuja

Mahauta da ke gudanar da sana’ar fawa a kwatar garin Suleja da ke Jihar Neja, sun koma mahautar Abuja da ke unguwar Deidei, a sakamakon takun saka da su ke yi da karamar hukumar yankin a sakamakon karin kudin haraji da ta yi musu.Mahautan wadanda su ka yi hijirar a ranar Juma’ar da ta gabata, […]

karin Haraji: Mahautan Suleja sun yi hijira zuwa Abuja
karin Haraji: Mahautan Suleja sun yi hijira zuwa Abuja

Mahauta da ke gudanar da sana’ar fawa a kwatar garin Suleja da ke Jihar Neja, sun koma mahautar Abuja da ke unguwar Deidei, a sakamakon takun saka da su ke yi da karamar hukumar yankin a sakamakon karin kudin haraji da ta yi musu.
Mahautan wadanda su ka yi hijirar a ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin ya kassara hada-hada a mahautar ta Suleja da kuma kawo karanci nama a garin, yayin da a gefe guda kuma ya bunkasa hada-hadarsa a mahautar ta Abuja.
Wani jagora a mahautar Suleja mai Suna Alhaji Ibrahim Baba, ya ce, kamar shekara biyu da su ka gabata, wani tsohon shugaban karamar hukumar yankin ya musu karin kudin yanka daga Naira 400 zuwa dubu daya a kan duk wata shaniya da za a yanka a mahautar, tare da alkawarin zai inganta mahautar wajen samar mata da ababan gudanar da ayyuka, “mun amince da karin, amma ba su cika nasu alkawaarin ba, inji shi.
Ya ce: “A kwanan nan, Shugaban karamar Hukumar na yanzu ya ce zai mana karin Naira dari 400 a kan dubu daya da mu ke biya da sunan zai yi mana rijiyar burtsatsai da kuma mashayan ruwa ta dabbobinmu a bangaren kara na mahautar. “Mun bukaci da ya gudanar da ayyukan tukuna kafin karin, amma bai amince ba, a sakamakon haka ya ba da umarnin a kama duk wani wanda ya yanka shanu da bai ba da kudin ba.
“Mu kuma mun san cewa dabbobi namu ne, to a maimakon a kamamu shi ya sa mu ka yi hijira zuwa mahautar Abuja da ke Deidei. Kuma an karbemu hannu biyu, duk da kasancewar mahautar ba ta hannun gwamnati kai-tsaye, ’yan kasuwa ne ke gudanar da ita, aiki a wajen ya fi mana rangwame a kan wannan ta hukuma, ga kuma saukin gudanar da aiki saboda akwai komai a can. San nan kashi 60 cikin 100 na shanu kamar dari biyu da hamsin zuwa dari uku da mu ke yankawa a duk yini a mahautar Suleja, mahautan da ke sayan su daga Abuja suke zuwa, kamar kashi 40 ne na Suleja suke saya,” a cewarsa.
A ganawarsa da Aminiya, shugaban karamar hukumar Suleja malam Ahmad Dikko Kassim, ya ce a sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya, ya zama wajibi gwamnatinsa ta nemo wasu hanyoyi da za ta inganta kudin shiganta kasancewar a yanzu haka biyan albashi a wajen sai an ci bashin Naira miliyan takwas a duk wata. “A zaman da muka yi da mai girma gwamna ya ba mu shawara uku, ta farko kan ko mu rage ma’aikata, ko mu datse wani kaso daga cikin albashin ko wane ma’aikaci, ko kuma mu kirkiro wasu hanyoyi na  samun karin kudin shiga.
“Mun tantance ma’aikata har sau uku ba tare da gano na bogi ba, duk da cewa a baya an dauki tarin ma’aikata na sonkai inda kowa ya yi ta kawo nasa alhali ba wani aikin da za su yi, ba zan iya rage yawansu ba, kuma ba zan zabtare kudin albashin wani ma’aikaci ba a kan dan abin da a ke basu, a saboda haka ne na dauki zabi na ukun kuma a bangaren mahauta na yi zama da shugabanninsu, mu ka cimma yarjejeniyar za su rika biyan Naira 300 daga baya ma suka nemi a a jiye shi a kan Naira 200, kuma mu ka amince.