karin jirgin zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya – Suleiman Lawan
A makon da ya gabata ne Kamfanin Zirga-zirgar jiragen sama na Azman Air ya kaddamar da wani sabon jirgi da ya sayo wanda zai rika jigila zuwa kasashen Afrika da sauran kasashen Turai da Amurka. Jirgin Mai kirar Airbox 330, wanda ke da karfin xaukar fasinjoji har 286 ya taso daga kasar Egypt inda ya […]
A makon da ya gabata ne Kamfanin Zirga-zirgar jiragen sama na Azman Air ya kaddamar da wani sabon jirgi da ya sayo wanda zai rika jigila zuwa kasashen Afrika da sauran kasashen Turai da Amurka. Jirgin Mai kirar Airbox 330, wanda ke da karfin xaukar fasinjoji har 286 ya taso daga kasar Egypt inda ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da misalin karfe 1:52 na rana.
Alhaji Sulaiman Lawan shi ne Janar Manaja na Kamfanin zirga-zigar jiragen sama na AZMAN ya yi wa Aminiya karin haske game da alfanun da jirgin zai haifar wajen ci gaban jihar inda ya ce samuwar jirgin karin samun aiki ne ga al’mmar Jihar Kano, haka kuma abu ne da zai havaka tatatlin arzikin kasa “A duk lokacin da aka samu karin wani abu a harkar kasuwanci, musamman na jirgi an san akwai karuwar samun aikin yi ga jama’ar Kano. Duk da cewa akwai ’yan wasu jihohin a cikin ma’aikatanmu, amma yawanci ’yan Jihar Kano ne masu rinjaye” Janar Manajan ya kara da cewa: “Haka kuma abu ne da kai tsaye zai kara bunkasa tattalin arzikin jiha da kasa gaba xaya. Ina ganin ko da mutum xaya ne aka cire daga cikin dubban mutane marasa aikin yi a kasa an yi nasara wanda kuma abin ba akan sa shi kaxai yake tsayawa ba domin za a samu wasu ximbin al’ummar da za su ci abinci daga abin da yake samu na albashi. Bayan ga samun akin yi ita kanta gwamnati kama da ga kan tarayya da jiha za su sami wani abu daga hakan domin aduk lokacin da jirgin ya fara tashi za a rika biyan gwamnati harajai da dai sauransu.”
A cewarsa ba wannan ne jirgin da zai fara zirga-zirgar kasashe waje ba, domin sun daxe suna jigilar kasar Saudiyayya.
“Dama can muna da jirgi da ke zuwa kasar Saudiyya, wanda mun daxe muna harkar jigiar alhazai da kuma ’yan umara, don haka wannan jirgin kari ne wanda zai kara bunkasa ayyukanmu domin har jigilar kasashen su Dubai da China za mu rika yi insha Allah,” inji shi.
Babban Manajan ya bayyana cewa da zarar jirgin ya gama samun amincewar fara zirga-zirga daga hukumomin da suka kamata, jirgin zai fara gudanar da zirga-zirga ba tare da vata lokaci ba.
Ina kira ga ’yan kasuwa da su kara ba mu haxin kai wajen ci gaba da yin hulxa da mu tare da yi mana gyara a duk lokacin da suka ga mun yi wani kuskure.
“Muna godiya ga jama’ar kasar nan gaba xaya, musamman ma ’yan kasuwa, domin ’yan kasuwa su ne iyayen gidanmu, idan babu su to babu mu. Kasancewar Xan Adam ajizi ne muna bukatar a duk lokacin da aka ga mun yi wani kuskure kofarmu a buxe take a gyara mana.”
Har ila yau Alhaji Sulaiman ya yi wa kwastomomin AZMAN albishir da cewa: “Kamar yadda aka sani jiragenmu suna da saukin farashi fiye da kowane jirgi. Haka kuma ta fuskar abinci muna samar da abinci mai inganci ga kwastomominmu, kama daga na gida har zuwa na kasashen waje.
Mun yi tafiya a jirgin Emirate zuwa Dubai sai muka ga abincinmu ya fi nasu inganci. Mun yarda da cewa a harkar kasuwanci a duk lokacin da ka rasa kwastoma a matsayinka na xan kasuwa kai ne ka yi asara ba shi ba, domin shi zai iya tafiya wani wurin ya samu wannan abIn da kake da shi. Don haka a kullum tunanimu mu kara kyautata tare da ingaanta ayyukanmu ta yadda za mu gamsar da abokan hulxarmu.”
Aminiya ta rawaito cewa a jawabinsa a lokacin bikin kaddamr da sabon jirgin Shugaban Rukunin Kamfanin Azman Alhaji Abdulmanafi Sarina ya sha alwashin bunkasa harkar jigilar jiragen sama waxanda za su rika tashi daga Kano zuwa kasashen ketare.
A cewarsa: “A matsayinmu na ’yan kasuwa za mu yi iya bakin kokarinmu akan dukkanin wani abu da muka ga zai janyo hankali al’umma su zo jihar don yin kasuwanci. Har kullum burinmu shi ne mu ga tattalin arzikin Kano da Najeriya ya bukansa.”
Har ila yau, Alhaji Abdulmanafi Sarina ya nemi goyon bayan al’ummar Jihar Kano domin haxa hannu wajen bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki.