Karin kasafin N894bn: Buhari ya nemi yardar Majalisar Wakilai

Shugaban Kasar ya ce kasafin na sayen makamai ne da kuma allurar rigakafin COVID-19.

Karin kasafin N894bn: Buhari ya nemi yardar Majalisar Wakilai

Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Wakilai.

Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Wakiali takardar bukatar amincewarta da karin kasafin N894bn domin sayen makamai da allurar rigakafin COVID-19.

Takardar neman amincewar da Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Talata ta ce karin kasafin ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman bukatu.

Sauran bukatun kuma za a sanya su a cikin kasafin shekarar 2022, wadda ake sa ran gabatarwa a watan Satumba, 2021.

Ta ce karamin kasafin zai tabbatar da samar da makamai da sojoji za su yi amfani da su wajen samar da tsaro.

Ragowar kuma za a yi amfani da su domin tabbattar da ganain an yi wa kashi 70% na ’yan Najeriya da suka cancanta allurar rigakafin COVID-19, daga yanzu zuwa shekarar 2022.