Karin kudin kujerar Hajji ya dama wa maniyyatan Najeriya lissafi

Wannan mataki ya dama lissafin maniyyata da dama inda wasu suka fara yunkurin neman Hukumar NAHCON ta dawo musu da kudadensu.

Karin kudin kujerar Hajji ya dama wa maniyyatan Najeriya lissafi

Maniyyata aikinHajji a Nijeriya sun shiga jimami da rudu bayan da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da karin kudin aikin Hajjin bana daga Naira miliyan hudu da doriya zuwa Naira miliyan 8.3.

A baya Hukumar NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudu su biya Naira miliyan 4 da dubu 899, yayin da maniyyatan Arewa za su biya Naira miliyan 4 da dubu 699.

Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.

Sai dai a daidai lokacin da ake sa ran rufe karbar kudin kujerar Hajji a ƙarfe 11:59 na dare a shekaranjiya Alhamis, kwatsama ranar Lahadi, sai Hukumar NAHCON ta sanar da cewa an kara kudin kujerar da Naira miliyan daya da dubu 900, saboda matsalar karyewar darajar Naira, inda yanzu kuɗin suka koma Naira miliyan 6 da dubu 800 kan kujera, ga wanda ya yi ajiya ko ya biya kudinsa tuntuni.

Sannan wadanda za su yi sabon biya kudin ya haura Naira miliyan 8, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Hajiya Farima Sanda Usara ta fadi a wata sanarwar a Yammacin Lahadin, tana mai cewa lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana, Dala ba ta yi tashin da ta yi ba a yanzu.

Hajiya Fatima Usara ta ce hukumar za ta rufe karɓar cikon kuɗin ne a yau 29 ga Maris, kuma daga wannan lokaci babu maniyyacin da za su saurara matuƙar bai biya kuɗin kafin lokacin ba.

Wannan mataki ya dama lissafin maniyyata da dama inda wasu suka fara yunkurin neman Hukumar NAHCON ta dawo musu da kudadensu na aikin Hajjin da suka biya.

Malaman addini da kungiyoyin farar hula, sun bukaci Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ceto maniyyatan kasar nan, la’akari da matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Binciken da Aminiya ta yi a Arewa da Kudu ya gano, kalilan din maniyyata ne suka shirya biyan karin kudin da aka yi musu. Kuma da dama cikin maniyyatan sun soma neman hukumomin jin dadin alhazai na jihohinsu su mayar musu da kudadensu.

Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kuɗin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiyya ta ba Nijeriya yayin da ’yan kasuwa suke da kujera 20,000.

Sanarwar ta ce sababbin waɗanda suke da son sayen kujerar daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe, za su biya Naira miliyan 8 da dubu 225 da 467.74 yayin da waɗanda suka fito daga sauran yankunan Arewa za su biya Naira miliyan 8 da dubu 254 da 464.74.

Waɗanda suka fito daga Kudu, za su biya Naira miliyan 8 da dubu 454 da 464.74. Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya ce, karin kudin aikin Hajjin da takaita lokacin biya da Hukumar NAHCON ta yi, ya yi matukar dama wa hukumarsa lissafi lura da cewa akwai makiyaya da yawa da suka kudirta sauke farali a bana.

Shugaban ya shaida wa Aminiya cewa babban abin da ya fi damunsu shi ne, yadda Hukumar NAHCON ta takaita lokacin cika Naira miliyan 1.9 a kasa da kwana biyar.

Ya ce, zuwa makon jiya kafin sanarwar karin kudin hukumarsa ta samu maniyyata 1,490 da suka biyan kudin kujera. Don haka yanzu ba su san yadda abin zai kasance ba a gaba.

Daga cikin malaman addinin Musulunci da suka fito suna rokon gwamnati ta dauki matakin rage kudin kujerar Hajjin bayan karin kusan Naira miliyan biyu akwai Sheikh Kabiru Gombe, wanda a lokacin Tafsirinsa na ranar Lahadi ya bukaci mahukunta su duba lamarin.

Haka Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi na cikin wadanda suka yi wannan kira, inda ya ce ya kamata malamai su haɗu domin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu magana ya duba lamarin maniyyatan.

Ya shaida wa BBC Hausa cewa: ‘’Mun san halin da kasa ke ciki da ma duniya, alhazan nan da za su je aikin Hajji za su yi wa kasa addu’a, ina fata malmai su hada kai, su samu Shugaban Kasa su gaya masa Allah da Annabi, kuma bai wa alhazan nan farashin Dala mai sauki ba zai cutar da Gwamnatin Tarayya ba.”

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya ce batun Dala da ake yi a kan talakawa yake karewa. ‘’Dala ta tashi ne a kan talaka, ba ta yi tashin gwauron zabo a kan masu hali ba, talaka ne yake dandana kudarsa.

’Yan majalisar Wakilai da Dattijai da ministoci da duk masu ba da shawara, su roki bawan Allan nan ya saukaka wa alhazai domin su tafi da farin ciki su dawo da murna,” in ji shi.

Tuni Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanar da amincewa da tallafin Naira dubu 500 ga maniyyata Hajjin bana da suka fito daga jihar, a wani yunƙuri na rage masu raɗaɗin ƙarin kuɗin kujerar da Hukumar NAHCON ta yi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na X.

Ya ce “Duk maniyyacin da ya yi rajista kuma ya biya kafin alƙalamin Naira miliyan 4.7 da Naira miliyan 4.5 a Hukumar Alhazai ta Jiha a yanzu zai biya Naira miliyan 1.4 maimakon Naira miliyan 1.9.”

To sai dai sanarwar gwamnan ba ta fayyace ko tallafin zai kasance ga dukkan maniyyatan jihar ba ne ko wadanda ba za su iya yin cikon ba.

Hukumar NAHCON da ta sanar da ƙarin kuɗin kujerar Hajjin dai ta bayyana cewa ƙarin bai shafi maniyyatan da suke ƙarƙashin tsarin adashin gata ba.

Hukumar ta bayyana haka ne ’yan kwanaki bayan fitar da sabon farashin kujerar Hajjin ga maniyyatan bana.

NAHCON ta ce ita ce za ta ɗauki nauyin biyan cikon kuɗaɗen maniyyatan da suka biya ta tsarin adashin gata abin da ke nufin maniyyatan ba za su biya ƙarin ko sisi ba.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana