Karin kudin lantarki: NLC ta rufe ofisoshin NERC
Kungiyar ƙwadago ta rufe ofisoshin Hukumar Wutar Lantarki (NERC) da na kamfanonin rarraba wutar domin nuna adawa da karin kuɗin da aka yi wa ’yan Najeriya
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta rufe ofisoshin Hukumar Wutar Lantarki (NERC) domin domin neman a janye karin kuɗin wuta da aka yi wa ’yan Najeriya.
A safiyar Litinin shugaban kungiyar, Joe Ajaeron, ya jagoranta jami’anta inda suka je suka rufe ofishin NERC da ke Abuja.
A Kaduna kuma NLC ta rufe ofishin kamfannin rarraba wutar lantaki ta Kaduna Electric, a wani bangare na zanga-zangar.
Haka ma kungiyar ta rufe ofishin NERC Jos, fadar Jihar Filato, inda ta hana ma’aikatan hukumar shiga ofisoshinsu domin domin gudanar da aiki.
Wakikinmu da ke Jos ya ruwaito cewa jami’an tsaro sun isa ofisoshin domin dakile tashin rikici ko karya doka da oda.
- Kotu ta kama mace mai damfara da sa hannun Abba Kyari
- NAJERIYA A YAU: Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga
Tun a ranar Lahadi kungiyoyin kwadago a Najeriya suka yi barazanar rufe ofisoshin NERC da na kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin Najeriya da nufin ganin an soke karin kudin wuta da aka yi.
Ninka kudin wuta da aka yi a watan Afrilu dai ya sha Allah wadai daga al’ummar Najeriya, inda daga bisani majalisar dokokin kasar ta ba da umarnin a soke.
NERC ta sanar da rage kudin da Naira 19 ga masu amfani da layin Band A wadanda da farko ta yi wa karin kudin kilowatt daga Naira 67 zuwa N225.
Ragin Naira 19 da NERC ta yi a makon jiya dai bai gamsar da jama’ar kasar ba.
’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa a kasar, wadda ta samo asali daga janye tallafin man fetur kafin daga bisani gwamnatin kasar ta janye tallafi a bangaren wutar lantarki.