Karin mutum 110 sun kamu da Coronavirus a Najeriya
A ranar Asabar an samu karin mutum 110 da suka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya. Kamar yadda ta saba duk rana, hakan na kunshe cikin alkaluman da hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta fitar a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba. Harin Zabarmari: Buhari ya jajanta kan kisan manoma 43 […]
A ranar Asabar an samu karin mutum 110 da suka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.
Kamar yadda ta saba duk rana, hakan na kunshe cikin alkaluman da hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta fitar a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.
Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 110 da suka harbu da cutar a jihohi 10 da suka hada da Legas (26), Abuja (23), Kaduna (20), Katsina (11), Ogun (7), Ekiti (6), Filato (5), Ribas (4) Kano (3) , Nasarawa (3) da Neja (2).
Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 67,333 a Najeriya yayin da tuni an sallami mutum 62,819 da suka warke daga cibiyoyin killace masu cutar.
Da wannan sabbin alkaluma da aka fitar, jihar Legas ce a kan gaba ta fuskar yawan masu cutar da suka kai 23,190 sai kuma Abuja a mataki na biyu da mutum 6,767 yayin da jihar Filato ta tuke a mataki na uku da mutum 3,857
Kazalika, alkaluman sun nuna jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,171 tun daga watan Fabrairun 2020 da ta bulla zuwa yanzu.