Karin mutum 324 sun kamu da Coronavirus a Najeriya

A ranar Juma’a an samu karin mutum 324 da suka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya. Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Najeriya NCDC ce ta sanar da hakan cikin alkaluman da ta fitar kamar yadda ta saba duk rana. Matsalar Tsaro: Za mu gana da Buhari — NGF ‘Addu’o’i ne za su kawo […]

Karin mutum 324 sun kamu da Coronavirus a Najeriya

Kwayar cutar Coronavirus

A ranar Juma’a an samu karin mutum 324 da suka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.

Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Najeriya NCDC ce ta sanar da hakan cikin alkaluman da ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.

Kamar yadda ta saba duk rana, hakan na kunshe cikin alkaluman da hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta fitar a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 324 da suka harbu da cutar a jihohi 11 da suka hada da Legas (115) da Abuuja (110) da Kaduna (57) da Taraba (9) da Akwa Ibom (8) da Filato (6).

Sauran jihohin su ne Bauchi (4) da Ekiti (4) da Kano (4) da Katsina (4) da Ribas (3).

Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 68,627 a Najeriya yayin da tuni an sallami mutum 64,467 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka.

Da wannan sabbin alkaluma da aka fitar, har ila yau jihar Legas ce a kan gaba ta fuskar yawan masu cutar da suka kai 23,660 sai kuma Abuja a mataki na biyu da mutum 7,101 yayin da jihar Filato ta tuke a mataki na uku da mutum 3,910.

A yayin da ba a samu karin wadanda suka mutu ba, alkaluman sun nuna jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,179 tun daga bullarta a watan Fabrairun 2020 zuwa yanzu.