Karin mutum 790 sun kamu da Coronavirus — NCDC

Mutum 2,195 sun mutu tun bayan bullar cutar karon farko a watan Fabrairun 2019.

Karin mutum 790 sun kamu da Coronavirus — NCDC

Wani jami’in kiwon lafiya yana daukar samfur a daya daga cikin cibiyoyin da aka kafa da taimakon NCDC a wasu al’ummun Yankin Babban Birnin Tarayya

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya, NCDC, ta ce mutum 790 sun sake kamuwa da annobar korona a fadin kasar.

Alkaluman da Hukumar ta fitar sun nuna cewa akasarin wadanda suka kamu a Jihar Legas suke, inda aka samu karin mutum 574 da suka harbu.

Akwai kuma Ribass mai mutum 83, sai Ondo mutum 38 da kuma Ogun mutum 31.

Jihar Oyo ma an samu mutum 23, Delta mutum 10 da kuma Abuja mai mutum 9.

Sauran jihohin da aka samu sabbin kamuwa da cutar sun hada da Ekiti mutum 7 da Edo 6, Osun 4, Anambra 2, Bayelsa 2 da kuma Filato mutum 1.

A halin yanzu jimillar adadin mutanen da suka kamu a fadin kasar sun kai 179,908, sai dai 166,203 sun warke.

Haka kuma, alkaluman NCDC sun ce mutum 2,195 suka mutu tun bayan bullar cutar karon farko a watan Fabrairun 2019.