Karin ’yan Najeriya 269 da suka makale a Afirka ta Kudu sun dawo gida
Wannan adadi ya ƙaru kan mutum 324 da suka dawo a baya, lamarin da ya sa adadin ’yan Najeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu ya kai 593.
Karin ’yan Najeriya 269 da suka nemi komawa gida sakamakon hare-haren kyamar baƙi a Afirka ta Kudu sun sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce mutanen sun dawo ne a jirgin Air Peace daga birnin Johannesburg, yayin da jami’an Gwamnatin Tarayya suka tarbe su a filin jirgin.
Wannan adadi ya ƙaru kan mutum 324 da suka dawo a baya, lamarin da ya sa adadin ’yan Najeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu ya kai 593.
Ma’aikatar ta ce har yanzu ana ci gaba da jigilar sauran ’yan Najeriya da suka nuna sha’awar dawowa gida, musamman gabanin wa’adin ranar 30 ga Yuni da gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanya wa baƙin da ba su da takardun zama a kasar.
- Matasa 5 sun rasu a hatsarin mota a Birnin Kebbi
- Manyan abubuwa 5 kan sabon tsarin NYSC
- Matar aure ta yi yinƙurin yi wa mijinta yankan rago a Kastina
Ta kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin Afirka ta Kudu domin kare rayuka da muradun ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar.