‘Karnuka 10’
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Ya ya shirin sallah? Tare da fatan kowa an yi masa dinkinsa yana jiran wannan ranar. A yau na kawo muku labarin wasu ‘Karnuka 10’. Labarin ya kunshi alfanun yin alheri. A sha karatu lafiya. Taku: Gwaggo Amina Abdullahi. Akwai wani Sarki yana da karnuka 10 mafadata sosai. Yakan hukunta […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Ya ya shirin sallah? Tare da fatan kowa an yi masa dinkinsa yana jiran wannan ranar. A yau na kawo muku labarin wasu ‘Karnuka 10’. Labarin ya kunshi alfanun yin alheri. A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi.
Akwai wani Sarki yana da karnuka 10 mafadata sosai. Yakan hukunta bayinsa da suka yi masa laifi da wadannan karnukan.
Rannan wani bawansa ya yi subutar baki ya fadi wani abin da bai kamata ba. Sai ran Sarki ya baci. Ya ce lallai sai ya sa karkukan sun hukunta shi. Wannan bawansa sai ya yi sauri ya fadi gaban Sarki yana neman gafara ya ce da shi “Ya Sarkin garin nan na yi shekara 10, ina maka hidima don Allah ka ba ni kwana 10 kafin ka hukunta ni.” Bayan da Sarki ya ji haka, sai ya amince.
Wannan bawan sai ya je wajen mai gadin wadannan karnukan ya ce ya taimaka ya bar shi ya kula da wadannan karnukan na kwana 10. Sai ya barsa. Yau shi ne yi musu wanka, ba su abinci da magani har suka saba.
Bayan kwanaki 10 Sarki ya sa aka dauko wannan bawansa din ya ce a jefa shi cikin wadannan karnuka. Abin ya ba shi mamaki sosai ganin yadda karnukan suka fara lashe shi.
Sai Sarki ya tambayi wannan bawansa ya akayi? Bawan ya ce ai ya musu hidima ne na kwana 10 ba su manta da shi ba sai, shi da ya masa hidima shekaru 10 a kan dan karamin kuskure har ya manta. Sai abin ya ba Sarki kunya ya ce “ kunce shi na yafe masa.”