Karnuka sun kashe uwa saboda gardama da ’yarta
Wata uwar ’ya’ya uku ta mutu bayan da karnukanta biyu jinsin Amurka suka kai mata farmaki, sakamakon ganin tana gardama da ’yarta. Matar mai suna Elayne Stanley mai shekara 44 ta samu raunuka ta hanyar cizon karnukan a gidansu da ke birnin Widnes a Karamar Hukumar Cheshire a Birtaniya. Ya rike numfashinsa tsawon minti 24 […]
Wata uwar ’ya’ya uku ta mutu bayan da karnukanta biyu jinsin Amurka suka kai mata farmaki, sakamakon ganin tana gardama da ’yarta.
Matar mai suna Elayne Stanley mai shekara 44 ta samu raunuka ta hanyar cizon karnukan a gidansu da ke birnin Widnes a Karamar Hukumar Cheshire a Birtaniya.
- Ya rike numfashinsa tsawon minti 24 a cikin ruwa
- An kama mutum biyu da kokon kan mutane cikin makabarta a Kaduna
Asalin karnukan mallakar mijin Elayne ne mai suna Paul Leigh, wanda bai halarci zaman sauraron karar da aka shigar da shi a kotu ba.
Tun a shekarar 2016 ce Kotu ta bai wa Paul umarnin ya killace karnukan tare da kula da su.
’Yar Misis Elayne mai suna Louise Smith ta bayyana wa kotun cewa, karnukan masu suna DJ Billy suna rayuwa ne da mahaifiyarta wato Elayne Stanley kimanin shekarar uku.
“Mahaifiyata tana tare da karnukan da ’ya’yanta biyu,” in ji Louise.
Louise ta ce ba ta da masaniyar cewa an yanke wa Mista Paul hukunci a shekarar 2016 kan daure kiwon karnuka masu hadari, wanda hakan ke nuna cewa, za a tuhume shi kan sakin karnukan ba tare da kulawarsa ba.
Ta kara da cewa, ta ziyarci mahaifiyarta a gida inda suka yi musayar zafafan kalamai sannan daga bisani ta gano cewa, bayan ficewarta da gidan namijin karen mai suna DJ ya ciji mahaifiyata a tafin kafarta.
Ta yi kokarin ta sakaya karnukan biyu a dakin dafa abinci (kicin) amma sai suka yi mata bore suka rika kai mata cizo.
“Dukkan su dai manyan karnuka ne biyu, ba zan iya kawar da su daga farmakin da suka kai wa Elayne ba,” a cewar Jason Lennox, jami’ar da ta jagoranci shigar da karar a ofishin ’yan sandan Cheshire.
Ta bayyana abin da ya faru kan farmakin da karnukan suka kai, inda ta ce wadannan karnukan tsaro ne ko gadi kuma suna iya fusata daga zafafan kalaman mutane lokacin da ake gardama.
“Karen DJ shi ne ya fara kai mata farmaki yayin da ta dauke karya Billy daga wajen, daga bisani suka sake haduwa wajen far wa Elayne har sai da ta mutu,” inji Jason Lennox.