Karon battar Atiku da Tinubu a zaben 2023
Kowanne ya kafu, baya tsoron kashe kudi, amma Kwankwaso da Peter Obi za su dagula musu lissafi
Bisa dukkan alamu, za a yi karon batta tsakanin Jam’iyar APC mai mulkin Najeriya da babbar jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben kasar da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Farfesa Kamilu Sani Fagge daga Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana dalilan da wannan karon batta da za a yi a zaben 2023 zai kasance mai zafi a tsakanin manyan jam’iyyun biyu.
“Zaben zai kasance ne tsakanin manyan giwaye biyu, Atiku da Tinubu, saboda kowanne daga cikinsu ya riga ya kafa siyasarsa a fadin Najeriya sannan sun dade suna hankoron hawa kujerar shugaban kasa kuma ba sa tsoron kashe kudi, kamar yadda aka gani a lokacin zaben fid-da dan takarar shugaban kasa,” kamar yadda masanin ya bayyana.
Kawo yanzu dai, bayan tsawon lokaci ana kwan-gaba-kwan-baya, a karshe dai Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da zaben dan takarar shugaban kasarta, wanda tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe.
A babban taron na APC, wanda ta kammala a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni, 2022, Tinubu ya lashe zaben fid-da gwanin da kuri’a 1,271, aka kuma mika mishi tuta a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a zaben 2023.
Wanda ya zo na biyu a zaben fid-da gwanin, wanda mutum 14 suka fafata, shi ne tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuri’a 316, sai Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da kuri’a 235 a matsayi na uku, sai Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello da ya zo na hudu da kuri’a 47, sannan Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuros Riba da kuri’a 37 da dai sauransu.
Tsakanin Atiku da Tinubu za a fafata
Da wannan nasara da Tinubu ya samu, za a yi karon batta tsakaninsa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda shi ne dan takarar kujerar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Bugu da kari, akwai ’yan takarar shugaban kasa daga sauran jam’iyyun siyasa 16 da ke Najeriya.
Aminiya ta kawo rahoto a baya cewa Atiku Abubakar shi ne ya lashe zaben fid-da gwanin dan takarar shugaban kasa da jam’iyyarsa ta PDP ta gudanar a ranar 28 ga watan Mayu, 2022.
Atiku Abubakar ya fito ne daga Jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas, shi kuma Tinubu ya fito daga Jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yamma.
Kowanne daga cikin ’yan takarar na APC da PDP ya haura shekara 70 a duniya kuma sun shafe sama da shekara 30 a harkar siyasar Najeriya.
A yayin da Atiku Abubakar ke da shekara 75 a duniya, shi kuma Tinubu shekarunsa 70.
Bayan wadannan ’yan takarar shugaban kasa biyu, masana na ganin akwai wasu manyan ’yan takara biyu wadanda kowannensu ba kanwar lasa ba ne.
Wadannan kuwa su ne dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, wato tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Mista Peter Obi na Jam’iyyar Leba.
Kwankwaso na da karfi da dimbin magoya baya a yankin Arewa maso Yamma, musamman a jiharsa ta haihuwa, Kano, wadda kuma ita ce jihar da APC ke bugun gaba da ita wajen samun kuri’u.
A daya bangaren kuma, Peter Obi na da karfi da kuma tarin magoya baya a yankinsa na Kudu maso Gabas.
Ba a batun su Kwankwaso —Farfesa Fagge
Amma da yake tattaunawa da wakilinmu, shehun malami a Fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero ta Kamo, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce karon battar da za a yi a zaben shugaban kasa na 2023 zai kasance ne tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana cewa duk da karfin da kowanne daga cikin Kwankwaso da Peter Obi ke da shi a yankinsa, abu ne mai matukar wahala wani daga cikinsu ya ci zaben.
Ya kara da cewa dokar da ta wajabta wa dan takarar shugaban kasa samun akalla kashi daya bisa hudu na yawan kuri’un da aka jefa a kashi daya bisa uku na jihohin Najeriya da Abuja, za ta sa da wuya Kwankwaso ko Peter Obi su kai bantensu a babban zaben na 2023.
Ya ce, “Zaben zai kasance ne tsakanin giwaye biyu, Atiku da Tinubu, saboda kowanne daga cikinsu ya riga ya kafa siyasarsa a fadin Nigeria sannan sun dade suna hankoron hawa kujerar shugaban kasa sannan kuma ba sa tsoron kashe kudi kamar yadda aka gani a lokacin zaben fid-da dan takarar shugaban kasa.
“Abin da zai iya faruwa shi ne za a yi ja-in-ja sosai a zaben, wanda kuma ke iya sa a yi amfani da kudi sosai a zaben saboda acikinsu babu wanda ke shakkar fitar da kudade, kuma kowannensu ya zaku da ya zama shugaban kasa.”
Sai dai kuma ya nuna kyamarsa ga siyasar kudi, domin a cewarsa, “Tana iya sa mutane su zabi mutumin da ba shi ya fi cancanta ba, sannan wanda ya ci zabe ta hanyar amfani da kudi zai iya yin watsi da mutanen da suka zabe shi, saboda abin da zai fara mayar da hankali a kai shi ne yadda zai mayar da kudaden da ya kashe domin cin zabe.”
Tasirin zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa
Da yake tsokaci a kan zaben 2023 da ke tafe, masanin Kimiyyar Halayyar Dan Adam da Zamantakewa a Jam’iyyar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya ce zaben zai yi zafi sosai ganin cewa Atiku da Tinubu manyan ’yan takarar da za su kara.
Ya ce lallai, “Akwai babban artabu, musamman ganin cewa shi (Tinubu) zai fafata da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP
“Su biyun, kowannensu gogaggen dan siyasa ne wanda samun dan siyasa mai irin kwarewarsu a wannan zamani sai an tina da gaske.
“Sun yi daidai da juna a bangaren tarin arziki da sanin jama’a da kafuwa da yawan magoya baya da iya dabarun siyasa da kuma son mulki.
“Da wuya a samu wani hadin ’yan takara da zai kai nasu zafi a cikin masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.
“Sai dai kuma ya danganci yadda suka bi da kuma irin sa’ar da suka yi a zabinsu na ’yan takararsu na mataimakin shugaban kasa.
“Abu na gaba shi ne hanyoyin da za su bi domin samun goyon baya da hadin kan kungiyoyi da daidaikun mutane masu muhimmanci, musamman wadanda ba su ji dadin yadda sakamakon zaben fid-da dan takarar shugaban kasa ya kasance ba.”
Dokta Abubakar Umar Kari ya ci gaba da cewa, ’yan takarar shugaban kasa biyu, Kwankwaso da Peter Obi na iya zama babban kalubale ga Atiku da Tinubu, ko kuma, akalla, su dagula musu lissafi ta hanyar rage musu yawan kuri’u.
“Peter Obi na Jam’iyyar Leba dan kabilar Igbo ne, kuma yana ta tarin masoya da magoya baya a kafofin sada zumunta.
“Mutanen yankin Kudu maso Gabas, musamman matasa da ’yan boko da sauran masu ra’ayin neman kasar Biafra, suna ganin shi a matsayin wanda zai share musu hawaye kan zargin da suke wa jam’iyyar APC da PDP na cewa sun mayar da su saniyar ware.
“PDP na bugun kirji da yankin Kudu maso Gabas wajen kawo mata kuri’u masu yawan gaske, amma yanzu hakan na fuskantar barazana saboda fitowar Peter Obi a Jam’iyyar Leba.
“A daya bangaren kuma Rabiu
Musa Kwankwaso na NNPP yan shirin kurdawa ya yi kane-kane kuri’u a yankin Arewa, inda APC ke da karfi ta ke kuma bugun gaba da shi.
“A halin yanzu NNPP ta yi nasarar zama makomar ’yan siyasar Arewa da sauran yankuna da aka yi wa ba daidai ba a APC da PDP.”
Shi ma da yake tsokaci kan yadda zaben shugaban kasa na 2023 zai kasance, Farfesa Hassan Salihu na Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Ilimi da ke Jihar Kwara, ya ce Tinubu shi ne dan takarar da ya yi daidai da ya fuskanci Atiku a zaben.
Sai dai ya ce abu ne mai wuya a halin yanzu a iya hasashen abin da zai faru a lokacin zaben na 2023.
“Fitowar Tinubu ya za sa a fafata sosai tsakaninsa da Atiku Abubakar, dan takarar PDP. Ba da jima da kammala taron ba, don haka, ba za a iya cewa ga wanda a tsakanin su biyun zai samu damar cin zabe ba,” inji shi.
Masanin Kimiyyar Siyasar ya bayyana cewa APC na da babbar damar sake cin zaben a matsayinta na jam’iyya mai mulki, amma akwai jan aiki a gabanta domin kuwa dole ne ta yi kokarin hada kan ’ya’yanta.
Shi ma da yake magana, Farfesa Sylvester Odion na Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Jihar Legas, ya bayyana cewa zaben 2023 zai kasance ne kai-tsaye tsakanin Tinubu da Atiku.
Ya ce, “Karawa ce tsakanin Tinubu da Atiku da suka fito daga manyan jam’iyyun biyu. A yayin da harkokin siyasa kankama, akwai yiwuwar faruwar da dama.
“Akwai kuma bukatar daukar matakai masu basira, wanda ya iya allonsa ya wanke, ya zama shi jama’a suka zaba a ranar zabe.”
Gwamnoni za su zabi abokin takarar Tinubu
A halin da ake ciki, mai magana da yawun Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu, Mista Bayo Onanuga, ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Legas din yana da wata yarjejeniya da gwamnonin Jam’iyyar APC domin zaben wanda zai zama dan takararsa na kujerar mataimakin shugaban kasa.
Onanuga, a hirarsa da tashar talabijin na Trust TV a ranar Larabar ya ce za a warware batun dan takarar mataimakin shugaban kasa cikin ruwan sanyi da Tinubu, dan takarar jam’iyyar APC.
Ya ce a lokacin da Tinubu ya gana da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC (PGF), ya yi musu alkawarin ba su mukamin mataimakin shugaban kasa.
Da aka tambaye shi kan yadda tsohon gwamnan Legas din zai hada kan sauran ’yan takarar da ya mayar wajen tunakarar jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023, Onanuga ya ce Tinubu mutum mai tafiya, hatta ga wadanda suka ci amanarsa.
A cewarsa, dan takarar ya yi alkawarin hada kan jiga-jigan jam’iyyar domin cimma nasara a matsayin tsinstiya madaurinki daya.
Atiku Ya Gana Da Gwamnonin PDP a kan Mataimaki
Aminiya ta ruwaito cewa gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi wata ganawa da Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, a Abuja.
Taron ya gudana ne a ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron na sama da sa’a biyu, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce taron na daga cikin ci gaba da tuntubar juna bayan kammala zaben fid-da gwani kan batun abokin takarar Atiku da kuma yadda za a hada kwamitin yakin neman zaben da za a yi domin kwato mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
“Yana daga cikin shawarwarin, ana kuma ci gaba da tuntubar gwamnoni a kan hakan,” in ji Tambuwal.
Tun da farko dai gwamnonin sun gana da Atiku da Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Dokta Iyorchia Ayu, na kusan awa daya kafin shugabannin su tafi.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Douyi Diri (Bayelsa), Bala Muhammed (Bauchi), Nyesom Wike (Ribaa), Samuel Ortom (Binuwai), Aminu Tambuwal (Sakkwato), Seyi Makinde (Oyo), Godwin Obaseki (Edo), Darius Ishaku (Edo). Taraba) da Ahmadu Fintiri (Adamawa).
Daga Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir, Abdullateef Salau, Itodo Daniel Sule, Baba Martins (Abuja), Clement A. Oloyede (Kano) & Abdullateef Aliyu (Legas)