Karon fadar Shugaban kasa da Gwamnoni Bakwai na PDP
Daga Yasir Ramadan Gwale Sanarwa ta karade ko ina cewar tsagin gwamnonin PDP guda bakwai da suka dare wa uwar jam’iyyar PDP za su gana, ko sun gana da Shugaban kasa. Kafin wannan ganawa an jima ana kai ruwa rana tsakanin wadannan Gwamnoni da fadar Shugaban kasa, har ta kai ga a makon jiya, shugaban […]
Daga Yasir Ramadan Gwale
Sanarwa ta karade ko ina cewar tsagin gwamnonin PDP guda bakwai da suka dare wa uwar jam’iyyar PDP za su gana, ko sun gana da Shugaban kasa. Kafin wannan ganawa an jima ana kai ruwa rana tsakanin wadannan Gwamnoni da fadar Shugaban kasa, har ta kai ga a makon jiya, shugaban tsagin nPDP, Alhaji Kawu Baraje ya bada wata sanarwa a dukunkune cewar sun hade da babbar jim’iyyar Hamayya ta APC. Tambayar da za mu yi a nan ita ce, shin Shugaban kasa ya gana da wadannan gwamnoni a matsayinsu na nPDP ne, ko kuwa a matsayin sababbin gwamnonin APC, ko kuma ‘yan kan-katanga? Duk da cewar Gwamnan Jigawa da na Neja sun bayyana matsayarsu game da sanarwar Baraje.
A shirin BBCHausa na Ra’ayi Riga, sun tattauna wannan al’amari na turka-turkar PDP. A cikin wannan tattaunawa, Mataimakin sakataren watsa labarai na PDP bangaren Bamanga Tukur, Abdullahi Ibrahim Jalo ya yi wata tambaya mai muhimmanci, amma aka kewaye ba a ba shi amsar tambayar ba, wato cewa: “Shin su wadannan gwamnoni sun shiga APC ne a matsayin sauya sheka daga PDP zuwa APC, ko kuwa hadewa ce irin wadda ANPP da ACN da CPC suka yi?” wannan tambaya tana da muhimmanci a yi bayaninta, amma cikin shirin aka kewaye mata. Da Baraje ya bayar da wannan sanarwa, Gwamnan Jihar Kano Alhaji Rabiu Kwankwaso ya yi wani bayani a BBC mai rudarwa kan cewa za su koma su tattauna da jama’arsu sannan su yanke matsaya; wannan ya nuna cewar kamar ba su shiga APC ba ke nan.
Dangane da ita waccan tambaya da Jalo ya yi, yana da kyau su ma APC su yi mana warwarar wannan al’amari, domin dai mun san cewar tsakanin ANPP da ACN da CPC da suka yi hadaka ba da baki suka yi ba, sai da kowacce ta mayar da satifiket dinta ga hukumar zabe, sannan hadewar ta tabbata. Don haka, su wadannan gwamnoni na nPDP sun dawo da nasu satifiket din ne ko an yafe musu, ko kuwa sauyin sheka suka yi? A daina tafiya da ‘yan Najeriya a dukunkune.
Me zai faru idan suka tabbatar wa Shugaban kasa cewar suna nan daram dam dam a PDP? Bukatunsu a bayyane suke ga al’ummar Najeriya, manyan bukatunsu guda biyu dai su ne na cewar (a) Dole Shugaban kasa ya ajiye batun tsayawa takara a 2015. (b) Dole a kori Bamanga Tukur. A nan ma za mu iya yin tambaya, shin wadannan Gwamnoni sun gamsu da yadda gwamnatin Jonathan ke tafiya ko kuwa kawai bukatarsu kada shugaban kasa ya tsaya zabe a 2015? Me ya sanya ba za su tsaya kai da fata wajen ganin shugaban kasa da Gwamnatin Tarayya sun yi wa al’ummar Najeriya ko Arewa Adalci ba? Sanin kowa ne Shugaban kasa yana nuna bambanci da zalunci tsakanin bangarorin kasarnan a bayyane, babu wanda ya yi haka, idan banda gwamnan Kano da na Kwara da suka yi batun rashin adalci a tsarin rabon arzikin kasa na Man da ake tonowa a cikin Ruwa da kuma wanda ake tonowa a kan tsandaurin yankunan da suke da man (Off-shore da On-Shore) Wannan korafin wadannan gwamnoni sun yi ne a kashin kansu tun kafin haifar da G-7.
Ko shakka babu irin wadancan bukatu su ne suka da mu al’ummar Najeriya. Dole a yi wa kowa adalci, a baiwa kowanne mai hakki hakkinsa, amma ga baki daya al’amarin PDP babu gaskiya a cikinta, da wanda yake zagin PDP da me yabonta duk ba masu gaskiya ba ne, illa nadiran in dai ‘yan PDP ne. Domin Atiku Abubakar da Abubakar Rimi babu irin abin da ba su kira PDP ba, amma kuma suka yi mata kome daga baya. Yana da kyau al’ummar Najeriya su fadaka cewa, PDP wani gungu ne na ‘yan MAFIA, babu wani wanda ya isa ya kauce daga tsarin da aka gindaya, dole dan PDP ya yi mata aiki yana so ko baya so, duk wanda ya ci ladar kuturu dole ya yi masa aski. Yana da kyau mu sani wadannan gwamnoni basa tayar wa PDP da hankali, illa kawai tashin hankalinsu shi ne kada darewar wadannan Gwamnoni ta haifar da barakar da PDP za ta rasa rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya, amma indai tafiya zasu yi daga PDP ana iya hada musu da gyaran Gwamnonin Kebbi da Katsina da Bauchi. Kayar da PDP ba abu bane mai sauki, domin rijiyar da ta cika da datti da dagwalo baza a taba iya yasheta daga waje ba, ya zama dole a shiga ciki a kwarfe ruwan da yake ciki sannan a samu ruwa mai kyau, ko kuma a cike ta a sake tona wata. Dan haka, gasa rago a murhun alade, ba zai taba haramta naman rago ba.
Yasir Ramadan Gwale [email protected].