KAROTA ta kama jabun magunguna na Naira miliyan 50
Mun samu nasarar cafke jabun magungunan ne a kan titin Murtala Mohammed da ke birnin Kano.
Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Kano (KAROTA) ta ce jami’anta sun samu nasarar cafke jabun magunguna na fiye da miliyan 50 a jihar.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar.
- ICPC ta shiga binciken badaƙalar sayar da guraben aiki
- Barayin da suka cinna wa Kasuwar Gombe wuta sun shiga hannu
A cewarsa, hukumar ta samu nasarar cafke jabun magungunan ne a kan titin Murtala Mohammed da ke birnin Kano “lokacin da direban motar yake ƙoƙarin shiga kasuwar Sabon Gari domin rabawa masu shaguna.
“Daga cikin magungunan da aka cafke sun hada da: maganin ciwon jiki, maganin zazzaɓi, maganin tari da sauran su.”
Shugaban Hukumar KAROTA, Faisal Mahmud Kabir ya ce hukumar ba za ta zuba ido ta bari ana ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar Kano ba.
Ya ja hankalin al’umma da su guji sayen magani a wajen da bai karanta ba domin gujewa fadawa cikin matsala.
Ya ce ƙofar hukumar a buɗe take wajen karɓar bayanan sirri domin daƙile yawaitar jabun magani a faɗin jihar nan baki daya.