KAROTA ta sallami jami’inta da ya fasa tayar tirela daga aiki

Hukumar ta sallami jami’in tare da mika shi hannun ‘yan sanda don zurfafa bincike.

KAROTA ta sallami jami’inta da ya fasa tayar tirela daga aiki

Shugaban Hukumar da ke Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan-Agundi, ya sallami jami’in hukumar Jamilu Gambo daga aiki.

An sallame shi ne ranar Alhamis, biyo bayan wata takaddama da ta faru tsakaninsa da wani direban wata babbar motar tirela, wanda hakan ya kai shi ga fasa tayarta.

Hakan ya sa direbobin motacin tirela rufe titin Kano zuwa Hadeja don nuna goyon baya ga abokin aikin nasu, wanda hakan ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin.

Sallamar tasa ta biyo bayan wani taron gaggawa da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano da hukumar KAROTA suka aiwarta tare inda suka cimma yarjejeniyar.

Shugaban na KAROTA, ya yaba wa Shugaban Kungiyar Masu Motocin Sufuri ta Kasa (NARTO) da jami’an ’yan sanda kan daukin da suka kai tare da hana lamarin munana.

A cikin wata sanarwa da kakakin KAROTA ya fitar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya roki afuwar jama’a a madadin Shugaban hukumar kan tsaikon da suka samu yayin zirga-zirga a titin.

Sannan hukumar ta sanar da cewar ta damka korarren jami’in ga ’yan sandan don zurfafa bincike tare da biyan direban tirelar asarar da ya yi masa.