KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano
Kwamishinan ya jaddada yadda harkar sufuri ke da muhimmanci wajen bunƙasar tattalin arziƙi a jihar.
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar.
Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su.
- Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai
- An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden
Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi.
Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma.
Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a faɗin jihar.
“Tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa da bunƙasar tattalin arziƙi. Don haka, gwamnatin jiha tana ɗaukar matakan da suka dace don inganta kayayyakin sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki a ciki da wajen jihar,” in ji shi.
Shanono ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 13.32 don aiwatar da wasu muhimman ayyuka a ɓangaren sufuri, ciki har da sayen sabbin motocin ofis da kuma gyaran motocin aiki na hukumar KAROTA.
Ya tabbatar da cewa Naira miliyan 250 za a yi amfani da su wajen sayen motocin ofis, yayin da sauran Naira miliyan 250 ɗin za a kashe su wajen gyaran wasu motocin aiki guda biyar.
Kwamishinan ya yi ƙarin haske kan yadda motocin da za a gyara za su laƙume kuɗaɗe daidai da kuɗaɗen sabbin motocin da za a siya.
“Waɗannan motocin aiki ne, kuma manyan motoci ne. Ba za a iya haɗa su da motocin ofis da shugaba ke amfani da su ba, domin suna da bambanci,” in ji shi.