KAROTA za ta tara Naira biliyan 1 a 2021

Hukumar Sufuri ta Jihar (KAROTA) ta bayyana kudurinta na tara harajin Naira biliyan daya a shekarar 2021. Shugaban KAROTA, Bappa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan yayin da yake kare kasafin hukumar a gaban Majalisar Dokokin jihar a ranar Litinin. An ba da damar shan giya da zina bayan yi wa Shari’ar Musulunci kwaskwarima a […]

KAROTA za ta tara Naira biliyan 1 a 2021

Wasu dakarun hukumar KAROTA

Hukumar Sufuri ta Jihar (KAROTA) ta bayyana kudurinta na tara harajin Naira biliyan daya a shekarar 2021.

Shugaban KAROTA, Bappa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan yayin da yake kare kasafin hukumar a gaban Majalisar Dokokin jihar a ranar Litinin.

Danagundi ya ce, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya amince wa hukumar ta dauki sabbin ma’aikata 1,400.

Ya ce a yanzu haka sun samu nasarar daukar sabbin ma’aikata 700, kuma nan da watan Janairun sabuwar shekara za su dauki ragowar 700.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa

Tags