Karroubi ga Khamenei: Ka daina dora wa kasashen waje laifin gazawarka

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mehdi Karroubi ya bukaci Shugaban Addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya daina dora wa wadansu laifi, ya tsaya ya dauki alhakin susucewar tattalin arziki da harkokin siyasar kasar. Mehdi Karroubi wanda ke zaman daurin talala a cikin gida na tsawon shekara bakwai ya bayyana haka ne a wata wasika […]

Karroubi ga Khamenei: Ka daina dora wa kasashen waje laifin gazawarka

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mehdi Karroubi ya bukaci Shugaban Addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya daina dora wa wadansu laifi, ya tsaya ya dauki alhakin susucewar tattalin arziki da harkokin siyasar kasar.

Mehdi Karroubi wanda ke zaman daurin talala a cikin gida na tsawon shekara bakwai ya bayyana haka ne a wata wasika da aka buga a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda kamfanin dillancin labarai na   Reuters ya ruwaito.

A wani abin da ba a cika gani ba, Karroubi ya zargi shugaban addinin mai tsattsauran ra’ayi da kama-karya, inda ya bukace shi ya sauya salon yadda yake jagorantar Ira tun kafin lokaci ya kure.

 “Kai ne babban jagoran Iran a tsawon shekara 30, amma har yanzu kana Magana kamar dan adawa,” Karroubi ya fadi a cikin budaddiyar wasikar da ya aike ga Khamenei kuma aka buga a kafar labarai ta Saham News, kafar labaran Intanet ta jam’iyyar masu ra’ayin sauyi ta Iran.

Ambatarsa da “dan adawa,” Karroubi yana nufin bai kamata Khamenei ya samu karfin iko ba, alhali yana sukar gwamnatin da aka zava ta Shugaba Hassan Rouhani ba, wani shugaban mai kazar-kazar da ke neman ’yanto tattalin arzikin Iran da ’yan boko daga sojojin Juyin Juya-Hali da sauran masu uwa a gindin murhu na kasar suka mamaye.

 “A cikin shekara 30, ka kawar da manyan dakarun juyin juya-hali domin ka aiwatar da naka tsare-tsaren, to yanzu sai ka fuskanci sakamakon haka,” inji Karroubi. 

Karroubi, mai shekara 80, kuma fitaccen malamin Shi’a kamar Khamenei da wani mai ra’ayin sauyi Mirhossein Mousavi sun tsaya takarar Shugaban kasa a zaven shekarar 2009 inda ya kasance daga cikin manyan mutanen da suka shirya zanga-zanga bayan Shugaba Mahmoud Ahmadinejad mai tsattauran ra’ayi ya sake lashe zaven da ake da yakinin an tafka magudi. Sai dai mahukuntan kasar sun musanta haka.

Karroubi da Mousavi da matar Mousavi, Zahra Rahnavard suna ci gaba da zaman daurin talala a gida tun shekarar 2011 bisa umarnin Khamenei. 

Shugaban Addinin shi ne Babban Kwamandan Askarawan Iran kuma shin ne yake nada shugaban kotun kasar, sannan ana zaven manyan ministoci ne ta hanyar shawartarsa, kuma shi ne ke da Magana ta karshe a kan harkokin kasashen wajen Iran da kuma shirinta na Nukiliya.

 Idan aka lura za a ga dan ikon da Shugaban kasar yake da ita bai taka kara ya karya ba.. 

Khamenei ya sha zargin gwamnatin Rouhani da gazawa wajen rage rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki da rashin daidaito. Kuma yakan dora wa ’yan majalisar dokokin kasar da tsofaffin shugabanninta da kuma kasashen yammacin Turai alhakin duk wani hali da kasar ta shiga.

Mahukunatn Iran masu tsaurin ra’ayi suna zargin Karoubi da zama “dan tawaye” kuma “maciyin amanar kasa.”

A wata wasika da Karroubi ya rubuta ga Rouhani a shekarar 2016, ya bukaci a yi masa shari’a a bainar jama’a ta yadda zai ji laifin da aka kama shi da shi, kuma ya kare kansa.