karshen danniyar PDP ya zo – Shugaban LP na Kalaba
Shugaban jam’iyyar Labour Party na mazaba ta daya da ke karamar Hukumar Kalaba ta Kudu, Alhaji Abdul Muhammad Musa Faruk, ya bayyana cewa da yardar Allah karshen danniya da rashin adalci, tare da mulkin dauki dora da jam’iyyar PDP ta saba yi a kasar nan ya zo karshe, musamman irin yadda nadin dauki dora ya […]
Shugaban jam’iyyar Labour Party na mazaba ta daya da ke karamar Hukumar Kalaba ta Kudu, Alhaji Abdul Muhammad Musa Faruk, ya bayyana cewa da yardar Allah karshen danniya da rashin adalci, tare da mulkin dauki dora da jam’iyyar PDP ta saba yi a kasar nan ya zo karshe, musamman irin yadda nadin dauki dora ya yi tasiri a jam’iyyar PDP , a zaben fidda gwani da ta yi a Kuros Riba kwanan baya.
Shugaban ya bayyana haka a ganawar sa da Aminiya jim kadan da tabbatar masa da shugabancin jam’iyyar LP a mazabar ta daya, a zaben shugabannin jam’iyyar da aka yi a wannan mako.
Alhaji Abdul Muhammad Musa Faruk, wanda aka fi sani da suna ‘Faro’ ya ce rashin adalci da aka nuna musu wajen zaben fitar da dan takara ‘lokacin muna jamiyyar PDP, ya sanya muka yi watsi da jam’iyyar muka fice mu da dan takarar mu, sanata Prince Bassey Out, wanda kowa yasan mutum ne mai jama’a, mai taimaka wa talakawa, wanda har wa yau babu ruwansa da nuna kabilanci, ko bambancin addini. Tabbas kowa ya sani hatta mu ’yan Arewa ma da muke mazabarsa ya yi mana alheri tunda idan kai ba ka samu ba wani naka ya samu”.
“Zan yi duk iyakacin bakin kokarina in ga mazabata ta daya, dan takarata ya lashe kuri’un da za a kada, musamman tunda dama mu jama’arsa ne, da aka hana masa takarar majalisar dattijai karo na uku, da masu ganin idan ba su ne suka nada mutum ba, ba zai kai labari ba. Abin da ya bakanta mana ke nan muka ce a sauya sheka, muka dawo labour party, yanzu shi ne zai yi mana takarar majallisar dattijai a wannan jam’iyya, inji shi. .
karshe ya bukaci sauran ‘yan jam’iyyun adawa su zubar da makaman su, su dawo jam’iyyar Labour party.
Dangane da manufofin jam’iyyarsa da dan takarasu, cewa ya yi: “Ga mai yi don talaka da kuma kishin talakawa, ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba. “.
Yawancin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu game da zaben shugaban jam’iyyar matakin mazaba sun bayyana zaben da aka yi wa Abdul Muhammad Musa anyi daidai, tunda dama ’yan jam’iyyar da dantakarar ta su ma’abocin jawo kowace kabila jikinsa ne, kuma anyi abin da ya dace.