karshen munafuncin Najeriya

Kowa ya san shugabancin Najeriya, musamman Soja da PDP su ne suka jefa mu halin da muke ciki yanzu, amma saboda rauni hatta wasu daga cikin malaman addini da ‘yan boko da sarakuna da attajirai da ‘yan siyasa duk sun zuba ido tamkar da su aka hada baki ake yin duk satar da ake yi […]

karshen munafuncin Najeriya
karshen munafuncin Najeriya

Kowa ya san shugabancin Najeriya, musamman Soja da PDP su ne suka jefa mu halin da muke ciki yanzu, amma saboda rauni hatta wasu daga cikin malaman addini da ‘yan boko da sarakuna da attajirai da ‘yan siyasa duk sun zuba ido tamkar da su aka hada baki ake yin duk satar da ake yi mana, ta mutane da dukiya da kisa da tsafe-tsafe da kowanne fajirci na saba wa Allah. 

Talakawa da abin ya fi cutarwa sun kasa haduwa su ce ba su yarda ba. Satar daruruwan ‘yan mata da matan aure da yankan rago da ake ta yi wa dalibai da magidanta, ga satar kudin gurbataccen mai da hana talakawa yin zanga-zangar lumana, sai malaman jami’o’i, da ma’aikata: Likitoci da ungozomomi. Duk wadannan ba sa tunanin masu mulki, na da dama yanzu kowannensu ya ci gaba da sharholiyar da yake yi, na fajirci da tsafi da kisa da sata da shaye-shayen ababen sa maye da haukatarwa. Shi yasa hukunta masu laifi ba zai yiwu ba. Kamar yadda na sha fadi duk abin da aka yi-aka yi a hana ya ki hanuwa, to masu ikon hanawar ne suke yi. Suke gurbata ‘yan baya (matasa) samari da ‘yan mata.
Al’umma ta fada wani hali na halaka, sai abin da Allah ya yi, idan har ba mu iya kawar da masu saba wa Allah daga mulki da shugabantar al’umma ko jagoranci ba. Musamman da ake samun limamai na addini da laifin lalata yara, maza da mata da matan aure. Abin ya watsu har a jami’o’i da makarantun kwana. An kasa hanawa saboda an kasa yi musu hukuncin da Allah ya ce a yi musu a bainar jama’a. Yanzu anzo makura ko dai masu ikon gyarawar su gyara ko mu dauki mataki akan su gaba daya, tare da abokan yin nasu.
Kamar yadda baci ba shi ne ya yi kansa ba, haka ma gyara ba zai yi kansa ba. Tilas sai wasu ma’abota gyara sun hadu sun gyara, ko a gamu da fushin Allah, irin yadda muke fama da annobar mutuwa a halin yanzu.
Idan shugabanni suka lalace, me ya kamata mu mabiya mu yi? Mu yi musu bara’a! duk wanda ka gani cikin inuwa wasune suka tsaya masa a rana. Bara’ace maganin azzaluman shugabanni. Wayau, yasan na ki! Idan suka ce ‘e,’ mu ce, ‘a’a’, idan suka ce wayyo – mu ce mun ki! Allah yasa mugane mu yi riko da igiyar Allah kada mu rarrabu. Allah yasa mu ne za mu gyara komai ameen, summa ameen.
Allah ba zai canza mana ba, har sai mu da kanmu mun canza; mun daina aikata zunubai, mun tuba ga Allah tuba na hakika, ba tuban Muzuru ba. Kowa ya ki ji ba zai ki gani ba!
Mutuna Allah ya ce, mafiya yawan mutane ba su da hankali, mafiya yawan mutane ba su sani ba. Duk wanda yake da hankali, ya kuma sani bai kamata ya daka ta mafiya yawa da Allah yace ba su sani ba, ko ba su da hankali. Ina hankali ga shugabannin da za su sace dukiyar kasar da suke mulki su kai wasu kasashe su boye, wai can yafi tsaro, yayin da su da ‘ya’yansu da matansu, har da iyayensu suke ciki rashin tsaro?
‘Yan jarida na kwarai su suka fi dacewa da isar da sakonnin mutanen kirki na samar da juyin-juya hali (cultural rebolution) ga sauran al’umma baki daya. Kwatankwacin irin yadda sahabbai suka rika samun sakonni daga Annabi (S.A.W) suna isarwa ga al’umma na ko’ina, birane da kauyuka a zamanin su, wannan shi ne cikakken misali. Annabin Allah da Allah yake aiko mala’ika gare shi, sai da sahabbai suka taimaka masa wajen isar da sakon Allah, saboda haka Allah ya tsara, da Allah ya ga dama ba sai wani ya taimaki Annabi ba zai samar da canji ga rayuwar al’ummar duniya.
Ana bin nagaba idan na gaban yana kan bin Allah (S.W.T), domin Allah shi ne abin bi na gaskiya. Masu kira da a rika yi wa shugabanni biyayya suna mantawa da yin kira ga shugabanni da su kasance masu bin Allah da Annabin Allah, matukar suna so ayi musu biyayya. Kada su kasance barayi, fajirai, matsafa, azzalumai da makamantansu. Aikata laifuka irin wadannan shi yake jawo annoba iri-iri. Allah ya fi kowa kishi! Duk wanda ba ya bin umarnin Allah, koda dansa ya yi wa umarni ba zai bi umarnin ba, ya kamata kowa yasan wannan. Shugabanni suji tsoron haduwa da fushin Allah, su kiyaye umarnin Allah, su yi adalci tsakanin kowa da kowa, ba tare da kowanne irin bambanci ba. Idan shugabanni ba sa bin umarnin Allah, sai a ki bin umarninsu, abi na Allah. Masu kira da a yi wa shugabanni addu’a, su rika yi wa shugabannin nasiha – kada su yi zalunci da fajirci da kisa da sata da karya ko yaudara.

Alh. AbdulKarim dayyabu,
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
(MOJIN) ta kasa baki daya
08060116666, 08023106666.