karshen-ti-ka-ti-ka-tik
A daidai lokacin da ranar Gwamnatin Shugaba Goodluck ke shirin faduwa sai ga Hukumar Albarkatun man Feturta kasa ta bayar da umurnin ci gaba da hakilon neman mai a harabar Tafkin Chadi ganin yadda al’amuran tsaro suka ingantu, bayan ta dauki dogon lokaci tana hake-hake a wurare sama da ashirin, amma ta ce ko naso […]
A daidai lokacin da ranar Gwamnatin Shugaba Goodluck ke shirin faduwa sai ga Hukumar Albarkatun man Feturta kasa ta bayar da umurnin ci gaba da hakilon neman mai a harabar Tafkin Chadi ganin yadda al’amuran tsaro suka ingantu, bayan ta dauki dogon lokaci tana hake-hake a wurare sama da ashirin, amma ta ce ko naso ba a gani ba. An yi amanna cewa da gangar ne aka ki kokartawa don hakan man da aka samu mai tarin yawa a gabar tafkin Chadi, wanda ya yi iyaka da kasashen Kamaru da Chadi. Haka nan kuma an hakikance akwai irin wadannan albarkatun a gaban kogin Komadugu Yobe, a dukkan wuraren da ya kurda ta Jihar Yobe, ya gangare cikin tafkin Chadin.
Dangane da haka ne ma aka samu man a yankin kasar Nijar da ke iyaka da arewacin Jihar Yobe.Tuni wadannan kasashen makwabta suka fara cin gajiyar albarkar man fetur din da ke nasu bangaren, na Nijeriya kuwa kutungwilar hukumomi ta hana a fara tonowa. To ba wadannan wuraren ne kadai Allah Ya tarfa wa garinsu nono ba, a Jihohin Bauchi ma da Gombe an gano dimbin albarkatun man, an kuma hakikance akwai shi a gabar kogin Binuwai. A ’yan kwanaki ma an gano arzikin man fetur kwance a wani yankin kudu-maso gabashin Jihar Kogi, aka kuma fahimci cewa Jihar Sakkwato na zaune ne dirshanshan bisa irin wannnan albarkar.
Amma a duk lokacin da aka ce an gano albarkatun mai a wani yanki na Arewa sai abin ya zame tamkar labarin kanzon kurege ga hukumomin gwamnatin tarayya, wadanda tono arzikin man da kuma sarrafa shi ya dogara a wuyansu. A gabannin karewar mulkin Ibrahim Idris, Gwamnan Jihar Kogi, an gano dimbin arzikin man fetur kwance a jiharsa, ya kuma gayyato kwararrun masana harkokin hakar mai, sun kuma tabbatar da haka, amma ba wani abin da aka yi don daukar matakan amfana da shi. Baicin haka nan kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wammako, ya taba tabo batun katarin da manema albarkatun karkashin kasa suka yi da danyen man fetur a Jiharsa. Amma baicin yayata wannan batun da ‘yan jarida suka yi, babu wani jami’in gwamnatin tarayya ko na kwamfanonin da suka gano albarkatun man fetur din da ya sanar da wanzuwarsa.
Duk da cewa gwamnatin tarayya ba ta cewa uffan game da dimbin arzikin man fetur da ake samu a daya daga jihohin arewa goma sha tara, sai ga shi Shugaba Goodluck Jonathan ya sanya Jihar Anambra cikin jihohin da suke da arzikin man fetur a matsayin ta goma, domin kuwa a cewarsa an gano mai a yankin Aguleri Otu da ke yankin karamar hukumar Anambra East, har ma an kafa wata matatar mai ta musamman don sarrafawa.
Idan kuma aka koma kan batun rashin mayar da hankalin gwamnatin tarayya game da rashin fara ayyukan hakowa da sarrafa dimbin albarkatun mai da aka gano a wurare da yawa a yankin arewa, sai a fahimci cewa ba a bukatar Arewa ne da karuwa da wannan arzikin. Manya-manyan kasashen Yammaci da Gabashin duniya sun kallafa ransu bisa wannan arzikin, kuma a sabili da haka ne ake ta bullo da take-taken da suka haddasa yamutsi da rashin kwanciyar hankali a dukkan wuraren da ake cewa an samu arzikin man fetur a wurare da yawa a yankin arewa-maso-gabashin kasar nan wadanda suka yi iyaka da sassan da aka samu man fetur a kasashen makwabta, kamar su Nijar da Chadi. Rige-rigen da Turawa ke yi don yin kaka-gida, su ji dadin tatsar wannan arziki a jihohin Barno da Yobe ne ke jawo fitintunun da ke wakana a wuraren, ana kuma jingina su da addini.
Kowa dai ya san cewa akwai albarkatun man fetur a arewa-maso-gabashin kasar nan, gwamnatin tarayya ma da kanta, da kuma kamfanin NNDC na raya yankunan arewa, sun bayar da kudi don bincikowa, an kai ga ganowa, amma an ki turzawa don fara hakowa. To ga shi nan ta bari al’amarin ya jawo wa al’ummomin yankin bala’i tun kafin su fara cin moriyarsa, kamar yadda man fetur ya zamewa kasar jangwam. Idan tun da farko da gaske Gwamnatin Jonathan ke yi game da kara kokartawa don binciken gabar kogunan kasar da ke kan iyakokin kasashen makwabta, musaman ma a arewa don gano albarkatun man fetur, to ai da ta fara da inda aka tabbatar mata cewa akwai dimbin albarkatun da aka ki tonowa, domin an ce a bari ya huce shi ke kawo rabon wani. Dangane da haka ne wasu manyan kasashen Yammacin Turai suka dukufa wajen haddasa fitintinu a yankunan Arewaci da aka tabbatar akwai albarkatun mai don su ji dadin tatsar wannan arzikin cikin ruwan sanyi.
To yanzu da yake an samu canjin da zai bayar da damar hako wanan arziki gadan-gadan, ko Yahudu da Nasara ba su so ba, ai ga shi nan Gwamnatin Jonathan wacce ke ta jan-kafa, tana bori da sanyin jiki, tana cewa ai an sha wahala a banza don neman mai a wannan yankin, ta ce lallai sai a ci gaba da batun nemowar don kada asirin kutungwilar da ta yi don hanawa ya bayyana.
Gwamnatin Janar Muhammadu Buhari ta sha alwashin hako arzikin man fetur din da aka ce yana nan dankare a harabar Tafkin Chadi da ke cikin kasarta, kuma hakan ne ya sa ta yi alkawarin wanzar da zaman lafiya a yankin da zarar ta danki ragamar mulki don afkuwar wannan abin alherin da zai kyautata rayuwar jama’ar yankin, ya kuma taimaka ainun wajen fafutikar raya kasa. Yanzu dai ana iya cewa karshen-ti-ka-ti-ka-tik tun da kutungwilar da ke hana tono albarkatun man Tafkin Chadi ta zo karshe.