karshen tika-tika tik
Karin maganar Hausawa da ke cewa karshen alewa kasa, ya yi daidai da yanayin babban taron da Shugaba Goodluck Jonathan ya kira da rana tsaka don tsara yanayi da manufofin da za su karfafa manufarsa da jama’arsa na mamaye fagen siyasa da kuma yin babakere a harkokin tattalin arziki da yin rub-da-ciki bisa dukiyar kasa. […]
Karin maganar Hausawa da ke cewa karshen alewa kasa, ya yi daidai da yanayin babban taron da Shugaba Goodluck Jonathan ya kira da rana tsaka don tsara yanayi da manufofin da za su karfafa manufarsa da jama’arsa na mamaye fagen siyasa da kuma yin babakere a harkokin tattalin arziki da yin rub-da-ciki bisa dukiyar kasa. To amma duk da cewa an yi zalunci da biye son zuciya wajen kauce wa tafarkin dimokuradiyya yayin da aka nannada wakilai maimakon jama’a su zabi wadanda suka san za su yi muhawara da yawunsu, aka kuma fifita wani bangare bisa wani game da adadin wakilan, duk da haka nan kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, hasali ma ana iya cewa dubban miliyoyin Nairar da aka narkar dangane da haka sun zama asara.
Tun tafiya ba ta kai ko ina ba aka fara fahimtar yadda bakin shugabannin taron ya karkata da kuma irin wainar da wasu wakilai ke toyawa, don a tabbatar an gabatar da manufofin da za su kyautata wa ‘yan shiyyoyin Kudu-kudu da kuma Kudu-masu-Gabas, al’amarin da ya nuna cewa an kirawo taron ne don biyan bukatunsu, sauran ‘yan Najeriya kuma suka kasance ‘yan rakiya, ko kuma a ce ‘yan a bi Yarima a sha kida. Gabannin kammala zaman babban taron, sa’ilin da aski ya zo gaban goshi sai abin boye ya fito fili game da manufar taron yayin da aka yi ta daddaga hakarkari tsakanin ‘yan Kudu da na Arewa, ana ta muhawara har da kumfan baki kan rabon arzikin kasa da kuma adadin da ya kamata a yarje wa jihohin da ake hakar man fetur. Rashin jituwa ta wanzu game da haka, sa’ilin da ‘yan Kudu suka nuna hadama da son kai, musaman ma wajen bayar da wata gurguwar shawara ta cire kananan hukumomi daga rabon rabon arziki kasa, alabarshi jihohin da suka ga za su iya su raba dukiyar da aka ba su tare da su. Taron kuma ya kawo wata shawarar kirkiro sababbin jihohi har guda 18 a matsayin toshiya ga wasu jihohin don bayar da goyon baya ga shawarwarin babban taron yayin da aka kai su gaban majalisun dokokin jihohi don amincewa.
To sai kuma daga karshe batun wani sabon kundin tsarin mulki da aka gabatar wa ‘yan majalisar, wanda kuma ba su san tushensa ko asalinsa ba, aka ce shi ne taron ya amince da shi don ya maye gurbin na 1999 wanda ake aiki da shi yanzu, kuma wannan kundin ya kunshi wasu batutuwan da aka tabbatar ba alheri ba ne ga wasu jinsin kasar nan. Wannan batun ya janyo tunzurin da ya rarraba kawunan ‘yan majalisar: ‘Yan Arewa sun nuna rashin amincewarsu da sabon kundin, ‘yan kudu kuma suka tsaya kai da fata sai a amince da shi. A lokacin da muhawara ta yi zafi, kawunan ‘yan Arewa da na ‘yan Kudu sun rarrabu, sai aka waiwayi shugaban taron, Mai Shari’a Idris Lebo Kutigi don a ji dalilin da ya sa ake neman halasta wancan haramtaccen kundin. Amma amsar da ya bayar ta kara tunzura masu adawa da kundin, domin kuwa cewa ya yi, “Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne ya umurce shi da ya tabbata an samar da wannan kundin tsarin mulkin, kuma idan har ‘yan Arewar da aka rinjaya a zauren taron ba su gamsu da haka ba, suna iya ficewarsu abinsu, su yi ta nuna adawarsu, kuma hakan ba zai hana a amince da haramtaccen kundin ba.
Wannan batun rashin dattaku da Mai Shari’a Kutigi ya gwada ya harzuka wasu wakilan taron kuma da ba don an kai zuciya nesa ba, da an aikata ta’asar da za ta wargaza taron, a watse ba girma, ba arziki. An dai amince a kawar da batun maye tsohon kundin tsarin mulki na 1999 da wanda aka tsara a asirce wajen taron da aka yi wa lakabi da “Sabon Kundin Tsarin Mulkin 2014,” aka kuma mayar da shi daidai da sauran shawarwarin da aka yanke wajen taron don yin gyara ga wancan kudin da ake so a canja.
Yanzu kasuwar taro ta ci, ta watse, an mayar wa Shugaba Jonathan da aniyarsa, sa’ilin da aka mika masa rahoton sakamako da bayanin bayan taron domin ya san na yi da shi. Amma sai dai ba zai yiwu ba ya nemi ‘yan Najeriya su yi zaben raba gardama don amincewa da abubuwan da sakamakon taron ya kunsa ba, domin sai an yi gyara ga sashi na 14 na kundin mulkin shekarar 1999. Abin da Shugaba Jonathan dai ya guda tun da farko, watau bi ta kan ‘yan majalisun tarayya don yin gyara ga kundin tsarin mulki, har ta kai shi ga kiran wancan taron da zai bayar da shawarwari game da haka, shi ne zai koma ta kansa, kuma ko ya ki, ko ya so, watau gabatar wa majalisun kasar nan kofen wadancan shawarwarin taron da aka mika masa don su huce haushinsu akan su. To ga shi nan tun daga yanzu mutanen Jonathan suna ta farfaganda don a tabbatar an yi zaben raba gardama kan abubuwan da sakamakon taron suka kunsa ciki har da wancan haramtaccen kundin tsarin mulki. Abin da ‘yan Najeriya ke cewa gami da haka shi ne bakin alkalami ya bushe, domin tun ana jin tika-tika, yanzu an ji tik.