Karuwanci ba alheri sai wahala – Safiya

Safiya Musa ’yar asalin Jihar Kaduna ce mai kimanin shekara 22 a duniya, wadda ta ce ta shafe sama da shekara daya tana zaune a Unguwar Tudun Wadan dan’iya da ake kira Bayan Gari a Bauchi. A tattaunawarta da wakilin Aminiya ta bayyana kadan daga cikin abubuwan da suka sa ta shiga karuwanci tare da […]

Karuwanci ba alheri sai wahala – Safiya
Karuwanci ba alheri sai wahala – Safiya

Safiya Musa ’yar asalin Jihar Kaduna ce mai kimanin shekara 22 a duniya, wadda ta ce ta shafe sama da shekara daya tana zaune a Unguwar Tudun Wadan dan’iya da ake kira Bayan Gari a Bauchi. A tattaunawarta da wakilin Aminiya ta bayyana kadan daga cikin abubuwan da suka sa ta shiga karuwanci tare da matsalolin da take fuskanta a halin yanzu:

Za mu so ki gabatar da kanki?
Sunana Safiya Musa na fito ne daga Jihar Kaduna sakamakon auren dole da mahaifina ya so ya yi min da wani mutum wanda ba na kaunarsa a cikin zuciyata, sanadiyar haka na zo Jihar Bauchi har na fada cikin wannan mawuyacin hali na sana’ar karuwanci. Ba zan bayyana maka sunan unguwarmu ba saboda wasu dalilai. Kuma na shafe sama da shekara daya ina zaune a Unguwar Tudun Wadan dan’iya da ke Bayan Garin Bauchi. Kuma sama da kasha 85 cikin 100 na ’yan matan da suke nan sun fito daga jihohi daban-daban har ma akwai ’yan kasashen Kamaru da Nijar. Babbar matsalar da ke sa ’yan mata shiga sana’ar karuwanci ita ce auren dole da wasu iyaye suke tilasta ’ya’yansu a wannan lokaci da muke ciki.
Da kika zo Jihar Bauchi iyayenki sun samu labarin inda kike?
Tabbas mahaifina ya samu labarin cewa ina zaune a Bauchi, ya yi in koma amma na ki komawa gida Kaduna saboda wasu dalilai na kashin kaina.
Nawa kike biyan kudin dakin da kike kwana?
Ina biyan Naira dubu daya a kowace rana, akwai kuma wadanda suke biyan Naira dubu daya da dari biyar har zuwa dubu biyu. Abin da kika samu a rana da shi za ki ci abinci sannan kuma ki biya kudin daki da sauran bukatu na yau da kullum. Ina addu’a Allah Ya kawo min ranar da zan fita daga cikin wannan sana’a ta karuwanci domin babu wani alheri a ciki sai wahala.
Kina amfani da kwaroron roba a lokacin saduwa?
Tabbas ina amfani da kwaroron roba a lokacin saduwa amma kuma akwai wasu maza wadanda ba sa amfani da mace da rigar kariya, dalilinsu shi ne ba sa jin dadin amfani da robar. Wani zai ce zai ba da Naira dubu biyu amma ba za a sa masa rigar kariya ba, kuma akwai dimbin mata da suke yarda da haka, ni kaina idan mutum zai ba ni Naira dubu biyu ba zan sa masa rigar kariya ba wannan shi ne gaskiyar abin da ke faruwa a tsakanin matan da suke da zama a wannan unguwa ta Bayan Gari.
Wadanne matsaloli kuke fuskanta a halin yanzu?
Babbar matsalar da muke fuskanta a halin yanzu ita ce ta rashin kudi, akwai mata da dama wadanda a rana ba sa iya samun Naira dubu daya domin ana fama da talauci da tsadar rayuwa a tsakanin al’ummar Najeriya.
Kina ganin mata masu zaman kansu a nan unguwar za su kai mutum nawa?
Gaskiya mata masu zaman kansu a Unguwar Bayan Garin Bauchi za ka samu sama da mata dubu biyu, domin kusan kullum sai ka hadu da sababbin fuska wadanda suka fito daga wasu jihohi sakamakon kuncin rayuwa saboda haka muna fatar Allah Ya shirye mu.
Idan kika samu wanda ya amince zai aure ki za ki daina karuwanci?
Ina tabbatar maka da cewa ko gobe na samu wanda zai aure ni tsakani da Allah zan tuba daga karuwanci domin babu wani alheri a karuwanci sai tsiya. A baya akwai wani saurayina da ya yi min alkawarin cewa zai aure ni daga bisani ya gudu ya koma jiharsa ta Gombe ko na kira shi a waya ba ya dauka.
Tsakanin ’yan mata da tsofaffin mata su wa suka fi shiga karuwanci?
A gaskiya sama da kashi 85 cikin 100 na masu shiga sana’ar karuwanci ’yan mata ne, sun fi yawa domin da yawa daga cikin maza ba sa son tsofaffin mata don haka duk lokacin da aka ga sabuwar budurwa a nan unguwar za ka ga maza suna yi mata layi kwana kadan kuma sai su koma kan wata sabuwar zuwa.
Shin za ki amince mu dauki hotonki a sa a jarida?
A gaskiya da mahaifina ba ya raye a duniya da zan amince a sa hotona a cikin wannan jarida ta Aminiya abin da ya sa kuma ba zan amince a sa hotona ba shi ne, matukar mahaifina ya ga hoton watakila sanadiyar haka ya kamu da ciwon zuciya, amma ina rokon iyaye don Allah su daina auren dole ga ’ya’ya mata a bar mu mu auri wanda muke so.
Shin kin taba zuwa asibiti a nan Bauchi domin a duba lafiyarki?
Duk kusan wata biyu ina zuwa babban asibitin Bauchi domin a duba lafiyata kuma an sha yi min gwajin cutar kanjamau amma ba a samun komai, muna fatar Allah Ya kare mu da sauran Musulmi baki daya lafiyata lau ba ni da wata matsala.
Wasu lokuta ne kika fi samun kudi?
Gaskiyar magana an fi samun kudi a lokacin sanyi domin mafi yawan maza sun fi fitina a lokacin sanyi, wasu kuma lokacin zafi kowa da yadda ya fi so, amma ni na fi samun kudi a sana’ar karuwanci a lokacin sanyi.
Mene ne sakonki ga matan da suke zaman kansu a nan unguwar?
Babban sakona ga daukacin ’yan matan da suke wannan sana’a shi ne mu ci gaba da addu’a Allah Ya kawo mana lokacin da za mu tuba daga wannan sana’a ta zubar da mutunci, domin kamar yadda na fada maka auren dole na daya daga cikin abubuwan da suke sa mata shiga sana’ar karuwanci. Kuma ko gobe na samu mutumin kirki wanda zai aure ni a shirye nake in tuba daga wannan sana’a. Bayan haka ina ba da shawara ga iyaye mata da maza a rage dogon buri a lokacin aure, domin akwai wasu iyaye wadanda idan mutum ya zo zai auri ’yarsu tsakani da Allah sukan sa dogon buri sakamakon haka sai yarinya ta lalace. Akwai wata kawata da saurayinta ya kai sadakin Naira dubu sai iyayenta suka ce kudin ya kasa sakamakon haka ta gudo daga garinsu ta zo Bauchi tana karuwanci har Naira 300 tana karba idan mutum ya zo dakinta. Idan aure ya yi tsada to tabbas karuwanci zai ci gaba da yaduwa a tsakanin al’umma, dole malamai da sauran al’umma su ci gaba da wayar da kan iyaye game da halin da muke ciki.
Daga karshe mene ne sakonki ga sauran jama’a?
Babban sakona shi ne ya kamata iyaye su sauya tunaninsu game da zamantakewar aure. Na biyu duk lokacin da yarinya ta nuna wanda take so to a hada su shi ne zaman lafiya. Kuma na yi matukar farin ciki bisa wannan dama da ka ba ni domin yin tsokaci game da halin da na samu kaina a rayuwa. Tun ina Kaduna nake ganin wannan jarida ta Aminiya na jima ina neman wakilin Aminiya sai yau da Allah Ya hada ni da kai, ina yi muku fatar alheri sannan al’umma su ci gaba da yi mana addu’a Allah Ya fitar da mu daga wannan sana’a ta karuwanci.