Karuwanci da kwaya za su bunkasa tattalin arzikin Italiya
Safarar kwaya da karuwanci da fasakwauri za su kasance cikin jerin al’amuran da ke bunkasa tattalin arzikin kasar Italiya a shekarar 2014, al’amarin da Cibiyar kididddiga ta kasar ta ce ya karu a kan na bara. An dai sake tsarin lissafin ne don dora kasar a kan tafarkin ka’idojin da Tarayyar Turai ta shimfida.Firayiministan kasar, […]
Safarar kwaya da karuwanci da fasakwauri za su kasance cikin jerin al’amuran da ke bunkasa tattalin arzikin kasar Italiya a shekarar 2014, al’amarin da Cibiyar kididddiga ta kasar ta ce ya karu a kan na bara. An dai sake tsarin lissafin ne don dora kasar a kan tafarkin ka’idojin da Tarayyar Turai ta shimfida.
Firayiministan kasar, Matteo Renzi, dan shekara 39, ya jajirce kan a takaita bunkasar tattalin arzikin kasar da kashi 2.6 cikin 100 a wannan shekarar, amma sai aka ga cewa idan aka bi kiddigar gurbataccen ciniki, wanda a da ba a lissafa shi, ai za a fahimci ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.
kasar Italiya ta yi fama da matsalar tattalin arziki a tsawon shekara 13, inda ta rika sarrafa dukiyar da kimarta ya kai Yuro tiriliyon daya da biliyan 560, a shekara biyu da suka gabata. Kuma a shekarar da ta wuce, an gano cewa tattalin arzikin ya yi kasa da kasha biyu cikin 100, in an kwatanta shi da na shekarar 2001, bayan an daidaita al’amura bisa la’akari da tsadar rayuwa. An daina gano cewa za a iya cike gibin matsalar tattalin arzikin ne ta hanyar kimanta yawan kudin da ake hada-hada da su a kasar, kan mummunan kasuwancin da ya hada da sarafar miyagun kwayoyi da fasakwauri da zaman badalar karuwanci.