Karuwanci: Shawarar da uwa ta ba diyarta

A wannan makon, wani labari ne mai kidimarwa kuma mai dauke da muhimmin darasi ya shiga komata. Ina kishingide, sai kawai na ci karo da wannan labari, wanda MALAM NASIR G. AHMAD KANO 08098559946 ya rubuta. Ni kuwaGizago na ce ba zan kyale shi haka nan ba, sai Gizagawa da sauran al’umma sun ji shi. […]

Karuwanci: Shawarar da uwa ta ba diyarta

A wannan makon, wani labari ne mai kidimarwa kuma mai dauke da muhimmin darasi ya shiga komata. Ina kishingide, sai kawai na ci karo da wannan labari, wanda MALAM NASIR G. AHMAD KANO 08098559946 ya rubuta. Ni kuwaGizago na ce ba zan kyale shi haka nan ba, sai Gizagawa da sauran al’umma sun ji shi. Ga labarin:


Wata budurwa ce ta nemi izinin mahaifiyarta, domin amince mata ta rika yin zina. Uwar ta nuna mata cewa wannan ba sana’ar arziki ba ce, abar kyama ce a al’adance, haramtacciya ce a addinance; amma yarinyar ta kafe kan ita dai tana so lallai uwar ta yarje mata, domin akwai tagomashin abin duniya mai yawa a ciki.

Uwar ta ce: “Tun da kin kafe sai kin yi, to zan amince miki amma bisa sharadin sai kin ci wata jarabawa da zan sa ki yi.” 

Cike da murna yarinyar ta ce ta yarda. “Shin mece ce jarrabawar farko?”

Uwar ta ce: “Gobe idan gari ya waye, ki je kofar fada, daidai inda sarki kan wuce. Idan ya fito sai ki yanke jiki ki fadi, ki sassandare kamar mai ciwon fyarfyadiya. Ki zo ki fada min abin da zai faru.”

Kashegari yarinyar ta je kofar fada, ta yi abin da uwar ta fada mata. Ai nan take sarki ya tsaya. Ya je wurin da ta fadi da kansa, ya sa aka tashe ta zaune. Sai da ta bude idonta, ta nuna alamar ta farfado, sannan ya tafi.

Cikin murna yarinyar ta koma gida, ta shaida wa mahaifiyarta abin da ya faru. Ta tambayi mece ce jarabawa ta biyu. Uwar ta ce, “Komawa za ki yi gobe, ki maimaita abin da kika yi yau.”

Kashegari ta koma, ta sake maimaitawa, amma sarki bai ko waiwaye ta ba, sai waziri ne ya je gare ta. Da ta nuna alamar ta farfado ya tafi. 

Ta koma ta fada wa mahaifiyarta, tare da neman sanin jarabawa ta uku. Uwar ta ce, “Wannan ce dai za ki koma ki maimaita.”

Da ta je ta yi a rana ta uku, sarki da waziri ba wanda ya kula ta, sai sarkin dogarai ne ya je gare ta, ya sa aka tashe ta zaune. Da ta nuna alamun ta farfado ya tafi abinsa.

Ta koma ta fada wa uwar yadda aka yi, tare da tambayar ko jarabawar ta kare? Uwar ta ce: “A’a, sai kin sake maimatawa sau uku tukuna.”

Yarinyar ta yi ta zuwa tana maimaita abin da ta yi a kofar fada. A rana ta shida sai ta je wa uwar tana kuka. Ta fada mata cewa, a rana ta hudu wasu mutane kadan daga masu wucewa ne suka je gare ta. A rana ta 5 kuma babu wanda ya kula ta. A rana ta 6 kuwa mutane ne suka yi ta zaginta, wasu ma har suna sa kafa suna shure ta, tare da gaya mata bakaken maganganu!

Uwar ta ce: “Madalla. To kamar yadda kika ga wannan al’amari, haka halin mazinaciya kan kasance. Komai kyanta da darajarta, a farkon lamari, sarakai da masu hannu da shuni ne za su rika tarairayarta. Daga nan sai su bar wa mabiyansu. A hankali darajarta na faduwa, har ta koma sai ya-ku-bayi ne za su yi hulda da ita. A karshe ma sai ta rasa mai kula ta, sai kaskanci da wulakanci da za ta rika fuskanta koyaushe. Wannan fa, idan har ta yi sa’ar ketare haduwa da miyagun cututtuka ke nan, wadanda za su karar da kazamin abin duniyar da ta tara. To yanzu zabi na hannunki. In har yanzu kina nan bisa ra’ayinki, sai ki je ki yi.”

Yarinyar ta ce: “Allah Ya kiyashe ni. Ai komai matsin rayuwar da zan shiga, ba zan yi zina ba.”

Uwar ta ce: “To Allah Ya yi miki albarka!”

Wayyo! Ka ji iyayen kwarai, masu shiryar da yaransu domin su zama nakwarai. Allah Ya ba mu sa’ar fahimtar gaskiya da ikon aiki da ita, amin! – Gizago.