karuwar masu kashe kansu da gangan
Rahotannin da ke fitowa daga kafofin watsa labarai sun nuna an samu karuwar mutanen da ke kashe kansu saboda wadansu dalilai na kashin kansu. Na baya bayan nan shi ne yadda aka tsinci gawar wani matashi mai suna Chinonso da ke kauyen Byazhim da ke yankin Kubwa na Babban Birnin Tarayya Abuja. An ce ya […]
Rahotannin da ke fitowa daga kafofin watsa labarai sun nuna an samu karuwar mutanen da ke kashe kansu saboda wadansu dalilai na kashin kansu. Na baya bayan nan shi ne yadda aka tsinci gawar wani matashi mai suna Chinonso da ke kauyen Byazhim da ke yankin Kubwa na Babban Birnin Tarayya Abuja. An ce ya kashe kansa ne bayan ya kwankwadi maganin bera. Rahoton ya nuna kafin matashin, dan kimanin shekara 21 ya kashe kansa, sai da ya bar wa mahaifiyarsa wasiyyar cewa ya yanke shawarar kashe kansa ne don ya “huta” da halin da ya tsinci kansa a ciki na kuncin rayuwa.
Sannan an sake samun rahoton yadda wani matashi dan kimanin shekara 32 mai suna Ogochukwu Ekwe wanda yake zaune a Unguwar Festac da ke Legas shi ma ya kashe kansa. Rahoton ya nuna matashin ya kashe kansa ne saboda kasancewarsa zabiya, wato kalar fatarsa ta fita daban da ta sauran mutane. Jama’a sun tarar da shi a mace ne bayan ya rataye kansa a gidan da yake zaune tare da mahaifansa da kuma ’yan uwansa. Rahoton ya nuna kafin ya rataye kansa sai da ya nuna wadansu alamu na shafe kwanaki ba tare da ya ci abinci ba. An ce ya yi haka ne don nuna bacin ransa a kan yadda mutane ke tsangwamarsa ko nuna masa kyama saboda yadda ya kasance zabiya.
Haka kuma an sake samun rahoton yadda wani mutum da ke da mata da yara hudu ya kashe kansa ta hanyar rataya a garin Oke Aro na Akure da ke Jihar Ondo. Marigayin da ake kira Dayo ya yanke shawarar kashe kansa ne saboda ya kasa daukar nauyin iyalansa. Marigayin da yake direban mota ne an ji yana yawan kokarin yadda yake samun sabani da maigidansa akan matsalar rashin bayar da balansa a lokuta da dama.
Sannan an samu rudani bayan an tsinci gawar wani magidanci dan kimanin shekara 27 a garin Onitea da ke Osogbo na Jihar Osun. Adesola Busari kamar yadda ake kiransa an same shi ne a mace bayan ya rataye kansa. Rahotanni sun nuna wani bankin bayar da kananan rance ne yake bin mamacin bashin, amma an tabbatar matarsa ta tallafa masa wajen biyan bashin. Hasalima saura Naira dubu 18 mamacin ya gama biyan bashin amma sai aka wayi gari ya rataye kansa. Haka kuma an samu labarin wani mutum mai kimanin shekara 50 a garin Dutse Makaranta da ke karamar Hukumar Bwari na Babban Birnin Tarayya Abuja da ake kira Tijjani da shi ma ya kashe kansa. Kafin nan, an ce marigayin ya taba yin aiki a Hukumar samar da ruwa ta Abuja (Water Board) a matsayin ma’aikacin wucin gadi. Tun bayan da aka sallame shi daga aiki shekaru da dama da suka gabata mutumin ya shiga halin tasku. An ce ya yanke shawarar kashe kansa ne bayan ya kasa ciyar da iyalinsa al’amarin da ya sa yake ganin yin haka a wurinsa abin kunya ne. Wadannan da ma wasu kadan ne daga cikin rahotannin da ake samu na yadda wadansu suke kashe kansu a sassan kasar nan.
Rashin warware matsalar da mutane ke fama da ita na daya daga cikin abubuwan da ke sa mutane su rika daukar rayuwarsu, kamar yadda masana kiwon lafiya suka sanar. Akwai dalilai masu yawa da suke sanya wa wadansu suke kashe kansu da gangan. Kadan daga ciki sun hada da mutuwar masoyi, ko sakin aure ko kwace ’ya’ya daga wajen ma’aurata walau a bangaren miji ko na mata ko yin fyade ko shan miyagun kwayoyi ko barasa ko cin fuska ko musgunawa ko kuma tsangwama. Haka kuma wasu kan dauki ransu saboda rasa aiki ko gida ko kudi ko samun rashin lafiya ko fitar da tsammani ko zaman kadaici ko yaki ko tabin hankali da sauransu.
Wasu daga cikin alamun da ke sanya a gane wani na yunkurin daukar ransa da gangan sun hada da rashin cin abinci ko rashin yin barci da kuma rashin yin cudanya da jama’a da yin tukin ganganci da yawan furta kalaman kashe kai da kyautar da dukiya babu wani dalili da ziyarar abokai da ’yan uwa sannan an ji ana furta kalmar “sai wata rana” da gudanar da binciken hanyoyin daukar rai da barin wasiyyar kashe kai da kuma sayen kayayyakin da ake amfani da su wajen kashe kai.
Idan ban da zamani ya canza, ba ya cikin al’adarmu a ji wani ya kashe kansa da gangan. Kashe kai mummunan dabi’a ce. Gwamnati da iyaye da kungiyoyin sa-kai da daidaikun mutane suna da rawar da za su taka wajen ganin an kawo karshen wannan mummunan dabi’a ta kashe kai. Da wuya ka ji wani ya kashe kansa ba tare da ya nuna alamar yin haka ba. Yakamata iyaye su yi taka tsan-tsan wajen tilasta wa yaransu yin wani abu da suka san ba sa so, musamman idan yaran nasu sun girma, sun mallaki hankalinsu.
Sannan akwai bukatar malaman addini su rika fadakar da mabiyansu a Masallatai da kuma a Coci-coci illar kashe kai. Su rika yin wa’azi game da muhimmancin yin hakuri da zaman lafiya ta hanyar tabo tarihin Annabawa yadda suka gudanar da rayuwarsu don fadakar da mabiya.
Haka kuma gwamnatin da ake gani ta gaza a kowane mataki a bangaren samar da ayyukan yi da samar da ilimi da na kula da lafiya yakamata ta zage damtse wajen samar da wadannan muhimman abubuwa ga ’yan kasa. Rashin haka ke sa wadansu ke yunkurin kashe kansu saboda takaici. Yakamata gwamnati ta bude ofishin sauraron koken al’umma a kowane lungu da sako na kasar. Yin haka zai sa a dauki daliban da suka yi karatu a bangaren sanin halayyar dan Adam samun aiki a orin wadannan ofisoshi da za a bude. Gwamnati za ta rage matsalar daukar rai ne idan ta bude wuraren shakatawa da suka hada da gidajen kallon talabijin kyauta da filayen wasanni iri-iri da kuma dakunan yin bincike da karatu don kawar da hankulan masu neman kashe kansu da gangan.