Karya Darajar Naira: Ɗangote ya faɗo daga mai kuɗin Afirka

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya faɗo daga matsayinsa na mai arzikin da yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirka sanadiyyar karyewar darajar Naira. Alhaji Aliko Ɗangote ya riƙe wannan kambin tsawon shekaru 12 amma yanzu ya koma na biyu, a cewar mujallar Forbes mai ƙididdige kuɗin masu arzikin duniya. Ɗan kasuwar Afirka ta […]

Karya Darajar Naira: Ɗangote ya faɗo daga mai kuɗin Afirka

Alhaji Aliko Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya faɗo daga matsayinsa na mai arzikin da yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirka sanadiyyar karyewar darajar Naira.

Alhaji Aliko Ɗangote ya riƙe wannan kambin tsawon shekaru 12 amma yanzu ya koma na biyu, a cewar mujallar Forbes mai ƙididdige kuɗin masu arzikin duniya.

Ɗan kasuwar Afirka ta Kudu, Johannes Rupert shi ne ya maye gurbinsa a matsayin maikuɗin Afirka.

Karya darajar Naira: Ba za mu janye labarinmu ba —Daily Trust ga CBN

Muhimman abubuwa kan Matatar Man Dangote

Rahoton da Forbes ta fitar a a ranar Lahadi yace Alhaji Aliko Ɗangote ya yi asarar fiye da $3.4 biliyan a rana guda sakamakon karyewar darajar Naira.

Sauran manyan masu kuɗin Najeriya su ma sun girgiza sakamakon karyewar Nairar.

Alhaji Abdulsamad Rabi’u, shugaban kamfanin BUA ya yi asarar $2.7 biliyan inda ya sauka daga matsayi na huɗu zuwa na shida a jerin masu kuɗin Afirka.

Babban Bankin Najeriya ne dai ya cire wa bankuna takunkumin cinikin Dalar Amurka, abin da ya haddasa faɗuwar darajar Naira.

Wannan ta sa a hukumance canjin ya kai N655/$1 saɓanin N471/$1 a farkon makon da ya gabata.

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos