Karya darajar Naira: Ba za mu janye labarinmu ba —Daily Trust ga CBN
Kafar Daily Trust ta yi watsi da da’awar bankin CBN da ke karyata rahoton kafar kan yadda bankin ya karya darajar Naira zuwa 631 a kan Dala daya
Daily Trust, daya daga cikin manyan kafofin yada labarai a Najeriya ya yi watsi da wata sanarwa da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da ke karyata rahoton kafar game da yadda a dare guda bankin ya kara farashin canjin Dala da kusan Naira 170.
A safiyar Alhamis Daily Trust da kuma Aminiya, daya daga manyan kafofin yada labarai na Hausa a Najeriya, suka wallafa wani rahoto cewa ranar Laraba Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba wa bankunan kasuwanci canjin Dala a kan Naira 631 a madadin kwastomominsu masu kasuwanci na kasa da kasa.
Bayan labarain ya tayar da kura, sai bankin CBN ya fitar da wata sanarwar cewa rahoton babbar kafar yada labaran ba gaskiya ba ne.
Sanarwar bankin ta yi ikirarin cewa, “Labarin cike yake da karairayi da kuma nuna rashin sanin yadda harkar cajin kudi domin kasuwanci na kasa da kasa ke gudana.”
- Za a biya ’yan majalisa masu barin gado biliyan 30 a matsayin ‘kudin sallama’
- Cire tallafi: Kwanan nan farashin mai zai sauko – NNPC
A kan haka ne kafar ta yi wa bankin martani cewa, labarin nata gaskiya ne kuma tana da hujjoji da ke tabbatar da duk abubuwan da rahoton ya kunsa, sannan ta kalubalanci CBN ya kawo nasa hujjojinsa da ke nuna sabanin rahoton.
Sanarwar da babbar kafar yada labaran ta fitar a yammacin Alhamis ta ce, “Muna nan a kan bakarmu cewa labarin namu gaskiya ne, kuma yana dauke da hujjoji uku na zahiri, da kuma karin haske guda daya.
“Na farko, CBN ya bayar da Dala a kan Naira 631 a ranar Laraba domin ’yan kasuwa da ke shiga ko fitar da kaya daga Najeriya; Na biyu, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da shirinsa na tabbatar da farashin canji na bai-daya; Ma uku kuma, Shugaba Tinubu ya gana da Gwamnan CBN a Fadar Shugaban Kasa. Wadannan duk hujjoji ne da babu ko tantama a kansu.
“Sannan, in ba gwamnati ba, kamar yadda take yi ta hannun CBN, wa ke da karfin ya kara Naira 169.4 a kan farashin canji na gwamnati a dare guda? CBN kadai ke hurumin yin hakan, ko ma da wane suna ya kira shi.
“Don haka muna nan a kan bakarmu cewa labarinmu gaskiya ne, kuma muna da hujjoji a rubuce daga muyanen da aka ba wa Dala a kan farashin da muka ambata.
“Saboda haka muna kalubalantar CBN ya kawo nasa hujjojin da suke nuna sabanin haka.
“Muna kuma jaddada cewa kafarmu ta Daily trust ba ta yada labaran karya, CBN da kansa ya san haka. Hasali ma, yanzu mun shekara akalla 25 a cikin jerin kafofin yada labarai mafiya kwarewa a aikin jarida da kuma kawo sauyi mai ma’ana a cikin rayuwar al’umma,” in ji sanarwa.
Ta ci gaba da cewa, “Yanzu haka, editanmu shi ne Gwarzon Edita a fadin Najeriya, sannan a watan Disambar 2023 wakilinmu ne ya lashe kambin Gwarzon Dan Jarida Mai Binciken Kwakwaf, kuma a watan da ya wuce mun lashe karin wasu kyaututtuka kan kwarewa a aikin jarida.
“Bugu da kari, kafarmu tana ba wa ’yan jarida horo, kuma duk inda suka je suna taka rawar gani, har a manyan wurare da ma’aikatu, ciki kuwa har da CBN.
“Yadda muka dade muna kawo wa al’umma sahihan labarai da kuma binciko musu gaskiya a aikace, shi ne abin da ya ja mana mutunci da samun karbuwa a wurin miliyoyin jama’a.
“Mu dai ba mu san abin da ya sa CBN karyata labarin ba, amma da mamaki yadda babban bankin zai jefi daya daga cikin kafofin da suka yi zarra a aikin jarida a Najeriya kamar mu, da irin wannan zargi.
“Amma har gobe muna nan a kan bakarmu cewa labarin da muka yi gaskiya ne.”