Karya doka

dan sanda ne ya kama wani Koje yana fitsari a daidai allon da aka rubuta cewa: “Laifi ne a yi fitsari a nan. Duk wanda aka kama, zai biya tarar Naira 500.” dan sanda: “Me ya sa kake fitsari a nan, ba ka ga allon nan ba?” Koje: “Don Allah ka yi hakuri!” dan sanda: […]

Karya doka
Karya doka

dan sanda ne ya kama wani Koje yana fitsari a daidai allon da aka rubuta cewa: “Laifi ne a yi fitsari a nan. Duk wanda aka kama, zai biya tarar Naira 500.” dan sanda: “Me ya sa kake fitsari a nan, ba ka ga allon nan ba?” Koje: “Don Allah ka yi hakuri!” dan sanda: “Sai ka biya tarar Naira 500 ko in tafi da kai.” Koje: “To ga Naira dubu daya, sai ka ba ni canji.” dan sanda: “Ba ni da canji, kara yin fitsarin sau daya a madadin canjinka.”
Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08098157899

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida