Karya mai baki biyu da kunne daya a fuska daya
Baki daya bai budewa da rufewa. An samu wata karya da take karin wani baki a fuskarta a Jihar Oklahoma da ke Amurka. Kuma halittar karya na sanya ta ciwo kamar yadda wanda ya mallaki karyar ya sanar. Baki biyu da karyar ke da su, ya maye gurbin kunnenta daya yayin da bakin ke da […]
- Baki daya bai budewa da rufewa.
An samu wata karya da take karin wani baki a fuskarta a Jihar Oklahoma da ke Amurka. Kuma halittar karya na sanya ta ciwo kamar yadda wanda ya mallaki karyar ya sanar.
Baki biyu da karyar ke da su, ya maye gurbin kunnenta daya yayin da bakin ke da hakora da zubar da yawu.
Wanda ya mallaki karyar ya sanya mata suna Toad, a birnin Oklahom. Jami’an kiyaye dabbobi sun gano cewa, karyar na da wata irin halitta na karin baki a gefen kunnenta.
Daga nan suka wuce da ita wajen kula da dabbobi zuwa sashen da ake yi wa dabbobi jinya a nan aka bar karyar da nufin bincike a kanta.
Shugaban Gidauniyar Kula da Dabbobi, Heather Hernandez da wanda ya mallaki karyar sun ce mun fahimce karyar ta bambanta da sauran karnuka, da farko karyar ta nuna alamar firgita amma da wanda ya mallake ta ya halarci inda aka ajiye ta sai ta nuna sanayya. Da farkon binciken likitan dabbobin na cibiyar da ya yi a kan karyar ya yi tunanin ko tana da karin kunne ne.
Likitan dabbobin ya ce, bayan gwaje-gwaje da aka yi wa karyar sai aka gano tana da kunne daya da baki biyu duk a kai daya.
Yadda karya Toad ke gudanar da rayuwa kamar sauran karnuka
Karin bakin Toad na janyo mata ciwo kamar yadda wanda mallake ta ya bayyana.
Heather, ya kara da cewa, da farko mun yi tunanin karin bakin da karyar ke da shi hakora biyu ne, sai da likitan hakora ya duba bakin sai ya ga akwai hakora da yawa a ka-rin bakin.
Wasu hakoran bakin sun karye bayan mun cire wadanda suke da matsala sai bakin ya zama kamar duk hakoran sababbi ne.
Binciken likitocin ba zai iya tabbatar da cewa, nan gaba ba za a iya samun matsala a daya bakin ba. Amma a yanzu duk za ta iya aiki da karin bakin kamar bakinta na asali ba tare da wata matsala ba. Bakin dai yana da lebba da kuma fitar da yawu kamar baki na asali, in ji Heather
Bakin da ya fito a gefen kunnen karyar bai da muka-muki don haka bai budewa da rufewa, fatar kunnen ce kawai ke rufe bakin.
Kamar yadda wasu karnuka da idan suka kai shekara biyar suke fama da larurar ciwo, ita wannan karyar ba ta da wata larura tana rayuwa ce kamar sauran karnuka.
Heather ya ce, “Wannan karyar ba ta ji da gani sosai da kuma tantace kanshi ko wari sosai saboda yanayin halittarta amma lafiyarta kalau.
Karyar tana son jama’ar da take tare da su, kuma da zarar ta shiga cikin ’yan uwanta karnuka sai su rika ba ta wuri saboda irin halittar da take da shi.