Karya ta cinye jinjiri dan wata 4 a Delta
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata karya ta cinye wani jinjiri a Jihar Delta bayan mahaifiyarsa ta bar shi a cikin mota, kamar yadda jaridar Leadership ta bayyana ranar Lahadi.Rahoton ya bayyana cewa mahaifiyar jinjirin mai suna, Maureen Akowe, tana tuda mota ne bayan daga bisani ta fita domin yi wa jaririn siyayya […]
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata karya ta cinye wani jinjiri a Jihar Delta bayan mahaifiyarsa ta bar shi a cikin mota, kamar yadda jaridar Leadership ta bayyana ranar Lahadi.
Rahoton ya bayyana cewa mahaifiyar jinjirin mai suna, Maureen Akowe, tana tuda mota ne bayan daga bisani ta fita domin yi wa jaririn siyayya a wani babban kanti da ke kan titin Okpanam na garin Asaba, inda ta bar karyar da yaron a cikin motar.
Kamar yadda wani wanda ya shaida faruwar lamarin ya bayyana, lokacin da Maureen take cikin shagon ne, karyar ta tasarwa jinjirin daga nan ne ’yar aikinta wadda ita ma take cikin motar ta yi ta kururuwa, amma kafin karasowar jami’an da ke tsaron shagon karyar ta riga ta farka cikin yaron, inda ta bar shi jina-jina. Daga nan ne aka garzaya da shi asibiti, inda daga bisani ya rasu.
Wata majiya ta bayyana cewa marigayin shi ne da daya tilo da Ubangiji Ya bai wa Maureen bayan aurenta da mahaifinsa shekara uku da suka wuce.
Mahaifin yaron wanda ya bukaci a sakaya sunansa, cikin hawaye ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin mai dakinsa ta bayyana abin da aikin shaidan, “har ila yau, aikin shaidan din shi ne zai sa na sallame ta daga gidana saboda na sha ja mata kunne kan karyar saboda wasu irin dabi’u da na ga tana yi, amma sai ta yi kunnen uwar shegu ta ce za ta nema masa magani,” inji shi.