Karya ta jira uwardakinta tsawon kwana 6 a asibiti
A farkon makon nan ne aka sada wata karya da uwardakinta bayan ta shafe tsawon kwana shida tana zaune a kofar dakin da aka kwatar da ita a wani asibiti da ke kasar Spain.Karyar mai suna Maya, wadda take da shekara biyu a duniya, ta zauna a kofar dakin da aka kwantar da uwardakinta mai […]
A farkon makon nan ne aka sada wata karya da uwardakinta bayan ta shafe tsawon kwana shida tana zaune a kofar dakin da aka kwatar da ita a wani asibiti da ke kasar Spain.
Karyar mai suna Maya, wadda take da shekara biyu a duniya, ta zauna a kofar dakin da aka kwantar da uwardakinta mai suna Sandra Iniesta, ’yar kimanin shekara 22 a duniya, har sai bayan da aka sallame ta daga asibitin mai suna Elda. Sandra ta yi fama ne da ciwon ciki yayin da suke tafiya da mahaifinta da kuma karyar a kan hanyarsu ta zuwa birnin Barcelona.
Daga nan ne suka garzaya asibitin Elda, aka kwantar da Sandra na tsawon kwana shida, inda aka yi mata aiki, kamar yadda jaridar The Independent ta bayyana.
A wannan lokaci ne mahaifin Sandra ya yi yunkurin komawa da karyar cikin mota don su koma masaukinsu, amma sai ta yi kememe ta ki barin kofar dakin da aka kwantar da Sandra.
Wadansu daga cikin ma’aikatan asibitin da suka fahimci halin da ake ciki, sai suka fara yada hotun Maya ta shafin sada zumunta na Facebook. Bayan haka ne, sai jama’a suka fara tururuwar ziyartar asibitin don yin ido hudu da Maya, inda wadansu daga cikinsu har da ba ta kyauta.
Yayin da aka sallami Sandra, manema labarai sun ji ta bakinta kan al’amarin, inda ta ce hakan ba wani bakon abu ba ne a gare ta. “Maya ta saba jira na duk lokacin da na shiga daki, ko makewayi. Ba ta barin wurin har sai bayan na fito,”inji ta.