Karya Ta Kashe Matashi A Kano
Mahaukaciyar karya ta hallaka wani matashi tare da jikkata wasu mutum hudu a garin Kano
Wata mahaukaciyar karya ta hallaka wani matashi mai suna Faruk Usman bayan ta gantsara masa cizo da wasu abokansa hudu a Jihar Kano.
Dan uwan marigayin da ya yi jinyar sa, Saddiku Usman, ya ce mutum guda daga cikin abokan yana kwance a asibiti, sauran kuma suna karbar magani.
- Abin da ya sa Tinubu da Atiku kasa ambaton jam’iyyunsu
- Hafsoshi 122 sun samu karin girma zuwa matsayin Janar
Saddiku ya ce, “Ni nake jinyar sa, ya kuma ce min sun tare karyar ne a titi suna kokarin rike ta, bayan mai ita ya zo karba, sai kawai ta hau cizon sa da wasu abokansa hudu.”
Tashar Freedom Radio Kano ta ruwaito Saddiku yana cewa likitoci sun shaida musu cewa jinkirin zuwa asibiti ne ya yi sandiyar rasuwar dan uwan nasa.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Dan Agundi Layin Maigasara da ke Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano kuma tuni aka yi jana’izar matashin.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akalla mutane 55,000 ne ke mutuwa kowace shekara sakamakon kamuwa da cutar cizon mahaukacin kare da sauran cututtuka masu alaka da hakan da ke yaduwa da kashi 99 cikin 100.
WHO ta ce rashin bai wa cutar muhimmaci da al’umma ke yi ne ya sanya adadin ke kara karuwa duk shekara a Najeriya.