Karyewar Farashi: Ba mu shigo da kayan abinci daga waje ba — Minista
‘Yan Najeriya dai na fatan farashin kayan abincin ya ci gaba da sauka ta yadda za a samu sauƙi.

Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni.
Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin gwauron zabo, daga bisani ta janye wannan shawarar.
- An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele
- Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu
Ministan ya danganta saukar farashin kayan abinci da ƙoƙarin manoma da suka koma gonaki a daminar bara, wanda ya sa amfanin gona ya yi yawa.
Ya kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashi domin jama’a su samu sauƙin rayuwa.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa saukar farashin kayan abincin na da alaƙa da wasu dalilai da suka haɗa da shigo da wasu nau’ikan kayan abinci daga waje ba tare da haraji ba.
Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya taimaka wajen ƙara wadatuwar kayan abinci a kasuwanni, lamarin da ke hana farashinsu tashi.
Har ila yau, ana cikin lokacin girbi, wanda ya sa manoma da yawa suka fito da amfanin gonarsu zuwa kasuwanni.
Yawaitar kayan abinci a hannun ’yan kasuwa ya rage farashin kayayyaki kamar shinkafa, gero, dawa, da wake.
Wani babban dalili da masana tattalin arziƙi suka bayyana shi ne, farfaɗowar darajar Naira a kasuwar musayar kuɗi.
Saukar darajar dala ya sa kayan abinci da ake shigo da su daga waje sun yi sauƙi idan aka kwatanta da watannin baya.
Tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka domin rage tsadar rayuwa, ciki har da sauƙaƙa shigo da abinci, sun taka muhimmiyar rawa wajen rage hauhawar farashi a kasuwanni.
Wannan mataki na ci gaba da samar da sauƙi ga jama’a yayin da ake fatan farashin kayan abinci zai ci gaba da yin ƙasa.