Karyewar Gada Ta Jefa Mu Cikin Matsala —Al’ummar Shongo Hamma
Karyewar gadar ta jawo cikas ga harkokin yau da kullum tare da hana zirga-zirga a yankin.
Al’ummar Shongo Hamma da ke yankin Tumfure a Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe sun shiga rudani sanadiyar karyewar Gadar Alhaji Bilya da ruwan sama ya yi a ranar 14 ga watan Yuni, 2024.
Karyewar gadar ta jawo cikas ga harkokin yau da kullum tare da hana zirga-zirgaa yankin.
Hakan ya sa al’ummar yin kira ga gwamnati da ta kai musu dauki domin ganin an gyara gadar da ta zama ita ce hanyar shiga garin.
Malam Abubakar Yahaya, daya daga cikin mutanen da abin ya shafa, ya koka da irin matsalolin da al’umma ke fuskanta tun bayan rugujewar gadar “da ya zama mana babban kalubale wajen aiwatar da ayyukanmu na yau da kullun.
- Alhazai sama da 900 sun mutu a Hajjin Bana
- NAJERIYA A YAU: Shin Ko Kalaman Kwankwaso Sun Kaɗa Hantar APC Ne?
“Muna kira ga gwamnati da ta taimaka mana wajen gina mana gadar cikin gaggawa domin rashin gadar zai kara katse hada-hada a yankin.”
Shi ma wani mazaunin yankin, Abbas Abdullahim, bayyana muhimmancin wannan gadar ga tattalin arzikin yankin inda ya ce yawancinsu sun dogara ne da gadar wajen jigilar kayayyaki da shiga kasuwanni, don haka, rushewarta ta yi tasiri sosai ga rayuwarsu.
Hakazalika, shi ma Malam Umar da ke zaune a yankin, cewa ya yi, karyewar gadar barazana ce ga harkar tsaron yankin.
A cewarsa, muddin ba a gaggauta gyara ta ba, yankin zai fuskanci matsala irin ta rashin tsaro.