Kasafin 2024: Gwamnan Gombe Ya gabatar da kasafin N207.8bn
Shugaban majalisar, Abubakar Muhammad Luggerawo ya ba wa gwamnan tabbacin cewa za su duba Kasafin cikin a kan lokaci.
![Kasafin 2024: Gwamnan Gombe Ya gabatar da kasafin N207.8bn Kasafin 2024: Gwamnan Gombe Ya gabatar da kasafin N207.8bn](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2021/11/IMG-20211111-WA0013.jpg)
Gwamna Inuwa Yahaya lokacin da yake gabatar da daftarin kasafin kudin ga Majalisa
A ranar Linitin ne Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya mika wa majalisar dokokin jihar kasafin Naira biliyan 207.8 domin shekarar 2024.
Kasafin kudin ya kunshi Naira biliyan 87.25 na ayyukan yau da kullum, da kuma Naira biliyan 120.5 na manyan ayyuka.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce kasafin kudin wanda shi ne na farko a wa’adainsa na biyu ya kara da cewa manufarsa ita ce dorawa daga inda ya tsaya a wa’adin mulkinsa na farko.
Ya ce zuwa watan Satumba an aiwatar da kashi 57.4 cikin dari na kasafin 2023.
- An binne mutum 80 bayan harin jirgin soji kan masu Mauludi
- Magidanta 340 sun sha duka a hannun matansu a Legas
Gwamna Inuwa, ya hori Majalisa da ta duba kasafin da idon basira ta kuma yi dukkan abin da ya kamata da zai dace da bukatar al’umma.
Da yake jawabi, shugaban majalisar, Abubakar Muhammad Luggerawo ya ba wa gwamnan tabbacin cewa za su duba Kasafin cikin a kan lokaci.