Kasafin 2025: Abba ya gabatar da N549bn ga Majalisa
Gwamnan Kano ya ware wa fannin ilimi kaso mafi tsoka a kasafin 2025
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar da Naira biliyan 594 a matsayin kasafin shekarar 2025 ga Majalisar Dokokin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa ɓangaren ne ya samu kaso mafi tsoka a kasafin na 2025.
Da yake gabatar da kasafin a ranar Juma’a, Gwamna Abba ya ce, kasafin ya sun ƙunshi Naira biliyan 312.6 na manyan ayyuka da kuma biliyan 236.5 na ayyukan yau da kullum.
Ya bayyana cewa hakan na nufin manyan ayyuka za su ɗauki kaso 57% na kasafin, ragowar kaso 43% kuma ayyukan yau da kullum.
Ya ce za a yi amfani da kaso mai tsoka na kasafin manyan ayyuka a kasafin wajen inganta rayuwar al’umma da inganta tattalin arziƙin Jihar Kano.
Ya bayyana cewa fannin da ware wa kaso mafi tsoka a kasafin shi ilimi wanda a Naira biliyan 168.
Sauran fannonin su ne:
Ilimi – Biliyan 168.
Hukumomin Gudanarwa – N98.2.
Kiwon Lafiya – Biliyan N90.6.
Samar da ababen more rayuwa – Biliyan N70.7.
Raya karkara – Biliyan N27.2.
Tsaro, shari’a da shirin gaggawa – Biliyan N23.5.
Aikin gona – Biliyan N21.0.
Matasa, matasa da Nakasassu – Biliyan N17.4.
Muhalli – Biliyan N15.6
Sufuri – Biliyan N12.8
Kasuwanci, masana’antu da yawon buɗe ido – Biliyan N3.9
Gwamnan Kano ya ce yanayin kuɗaɗen da aka ware wa kowane fanni a kasafin ya nuna irin muhimmancinbda gwmanatinsa ta bayar wajen inganta rayuwar al’umma da samar da ababen more rayuwa.
“Kamar yadda muka yi alkawarin inganta ilimi, duk da ƙarancin kuɗaɗen da mu ke sa su, ina shaida wa Majalisa cewa muna duba yiwuwar farfaɗo da Hukumar Tallafin Bunƙasa a ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi.
“Manufarmu ita ce samar da nagartacciyar hukuma da za ta ɗauki gabarar samar da taffinin inganta makarantun matakin farko da sakandare da kuma koyi da Gidauniyar Kula da Manyan Makarantu (TETFUND) domin samar da manyan makarantun jihar Kano” in ji shi.