Kasafin kudin badi da Shugaba Buhari ya gabatar zai amfani talaka kuwa?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin badi a gaban Majalisar kasa na kimanin Naira triliyan 8.6. Tun bayan da Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin, mutane suna ta sharhi a kan makudan kudin da shugaban ya gabatar, da yadda aka batar da kasafin kudin bara. Wannan […]

Kasafin kudin badi da Shugaba Buhari ya gabatar zai amfani talaka kuwa?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin badi a gaban Majalisar kasa na kimanin Naira triliyan 8.6. Tun bayan da Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin, mutane suna ta sharhi a kan makudan kudin da shugaban ya gabatar, da yadda aka batar da kasafin kudin bara. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane a kan ko dai wannan kasafin kudin zai amfani talakan Najeriya, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Zai amfani talaka fiye da ko wane kasafin –Alhaji Rabi’u Sani

Daga Adam Umar, Abuja

Alhaji Rabiu Sani: “Kasafin kudin zai amfani talaka fiye da kowane kasafin kudin kasa da ya gabata, kasancewar an sami karin zaman lafiya sannan an fara fita daga kangin matsalar tattalin arzikin kasa. Sannan da dama daga cikin ’yan gudun hijira da ke sansanonin gudun hijira na komawa garuruwansu za su kama sana’a su kula da kansu sabanin baya inda gwamnati ce ke daukan dawainyarsu.

 

Zai amfani talaka sosai idan ’yan majalisa ba su gurbata shi ba – Malam Sa’adu Usman

Daga Adam Umar, Abuja

Malam Sa’adu Usman: Kasafin kudin zai amfani talaka sosai idan ’yan majalisa ba su gurbata shi ba. Na ga yadda Shugaban kasa ya sako ayyukan tituna masu muhimmanci da sauran abubuwa da za su taimaki talaka ya bunkasa harkokinsa. Sannan kuma gashi kudin man fetur sai kara daraja ya ke yi a kullum wanda hakan zai taimaka wajen samar da kudin shiga ga gwamnati ta sauke nauyin alkawuran ayyuka da ta yi wa talaka.”

 

Zai amfani talaka idan ‘yan majalisa sun amince da kasafin – Isa Teacher

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Isa Teacher: “Kasafin kudin zai amfani talaka muddin idan ‘yan majalisun sun amince da kasafin da shugaban kasar ya gabatar musu. Misali akwai aikin wutar Mambila kai tsaye aiki ne da ya shafi talaka da idan aka yi za a samu alfanunsa. Sannan akwai ayyukan yi da aka shirya za a samar don talakawa kuma idan aka yi su za a rage zaman banza a tsakanin al’umma musammam matasa.

 

Zai taimka wajen dawo da walwala tsakanin ‘yan kasuwa  Zainab Sada

Daga Rabilu Abubakar, Gombe.

Zainab Sada (Zee Sada): “kasafin kudin zai taimaka wajen dawo da tattalin arziki da sanya walwala a fuskar ‘yan kasuwa da masu kananan sana’oi. Kasafin kudin kamar Shugaba Buhari ya duba zuciyar ‘yan Najeriya ne ma kafin ya gabatar, saboda ana cikin matsanancin halin rayuwa. Kuma muddin ‘yan majalisa suka yarda da kasafin, za a yi walwalar da zai sa a mance da kuncin da ake ciki na rayuwa.

 

 

Zai amfani talaka idan an yi aiki da shi –Abubakar Haruna

Isiyaku Muhammed

Abubakar Haruna: “A ganina duk shekara idan ka duba daftarin kasafin kudin, za ka ga cewa akwai bayanai masu kyau. Amma a kullum matsalar it ace aikin da kasafin yadda ya dace. Don haka ina ganin idan har da gaske za ayi amfani da abin da aka rubuta, to lallai kasafin zai amfani talaka. Don haka ina kira ga shugabanni da su tabbatar sun yi aiki da abin da suka rubuta, domin talaka ya gani a kasa.”

 

Ba zai wani amfani talaka ba  –  dan autan Kwankwasiyya

Isiyaku Muhammed

Mubarak dangarba: “Dubi da kasafin kudin shekaran da ta gabata. Gaskiya zan iya cewa. kasafin kudin wannan shekaran ba zai amfani talaka ba. Domin kuwa ko da an amince da kasafin kudin, ina mai tabbatar maka da cewa talakawan kasar nan ba za su gani a kasa ba.”