Kasafin kudin bana:-`Yan kasa na zaman jiran ganin canjin

daya da daya, idan ka ce hayaniyar yaki da cin hanci da rashawa da mahukuntan kasar nan su ka shiga, tun bayan zuwan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun bara, yau kusan shekara daya, ko kusa ba kai ta irin wadda gwamnatin ta shiga ba a kan kasafin kudin bana ba, […]

Kasafin kudin bana:-`Yan kasa na zaman jiran ganin canjin
Kasafin kudin bana:-`Yan kasa na zaman jiran ganin canjin

daya da daya, idan ka ce hayaniyar yaki da cin hanci da rashawa da mahukuntan kasar nan su ka shiga, tun bayan zuwan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun bara, yau kusan shekara daya, ko kusa ba kai ta irin wadda gwamnatin ta shiga ba a kan kasafin kudin bana ba, to, kuwa ba wanda zai ce ka yi karya. Ba don komai ba, sai don hukumomin da su ke yaki da cin hanci da rashawa irinsu Hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta`annati ta EFCC da Hukumar da`ar ma`aikata CCB da Kotunta CCT da sauran hukumomi, duk abin da suke yi su ta shafa, ba wata kwakkar shaidar da ake da ta ita da take tabbatar da cewa da hannun Shugaba Buhari a cikin yadda suke gudanar da ayyukansu, amma kasafin kudi kai tsaye ya shafi shugaban kasa, kamar yadda muka gani a bana, bisa ga dambarwa da cacar bakin da aka yi ta yi tsakanin bangaren  zartarwa, wato ofishin shugban kasa da bangaren `yan Majalisun Dokoki na kasa, kai har ma da al`ummar kasa, musamman masana tattalin arzikin kasa a kan kasa zartar da kasafin kudin na bana.
Daga karshe dai bayan kusan watanni biyar ko mu ce tun ranar 22 ga watan Disambar bara, da Shugaban kasa Muhammadu Bahari ya mika wa zaman hadin gwiwar Majalisun Dokokin na kasa, kundin kasafin kudin bana da ya kunshi sama da Naira tiriliyan shidda (=N=6tiriliyan), sai ya zuwa ranar juma`ar da tagabata 06-05-16, ta tabbata shugaba Buhari ya rattafa wa kundin hannu, wanda hakan ya kawo karshen wancan ka-ce-na-ce a kan kasafin kudin na bana, al`amarin da ya sa yanzu kundin kasafin kudi ya zama doka. Ko da wata takaddamar za ta sake tasowa tsakanin bangarorin biyu ba za ta wuce irin yadda bangaren zartarwa zai aiwatar da shi, aiwatarwar da Majalisun Dokokinke da wuka da nama na tabbatar da an ana aiwatar da shi sau da kafa kamar yadda suka zartar. Don haka ne ma aka ji shugabanMajalisar Dattawa Dokta Bukola Saraki yana shan alwashin za su zuba idanu sosai da sosai kan yadda bangaren zartarwar da kasafin kudin.
Kamata ya yi in yi wa mai karatu `yar matashiya a kan irin dambarwa da cacar bakin da aka shiga akan kasafin kudin banan, wanda shi nekaro na farko irinsa da aka taba samun hakan karara tsakanin bangarorin biyu, a cikin tarihin mulkin dimokuradiyya da kasar nan take kai yau shekaru 17.
Da farko dai bayan gabatar da kasafin kudin, sai ga labari ya fito daga bangaren Majalisar Dokoki cewa, kundin kasafin kudin ya bace bat. Can kuma bayan wannan ce-ce-ku ce ya lafa har, an fara muhawara akan kundin a majalisun, sai ta fara bayyana ana samun sabanin bambance-bzmbancen alkalumma yawan kudin a kan abin da ke cikin kundin da ke gaban Kwamitocin Majalisun Dokokin da kuma wanda ministoci suka riko suka zo, don kare kasafin kudin ma`aikatu da  hukumominsu. Duk wannan dambarwa da aka shiga kamar yadda na taba fadi a wannan fili, ba ya rasa nasaba da irin fadan da a ke yi tsakanin gaskiya da karya, da neman yadda za a gyara barnar da ake yi shekaru aru-aru.  
Tun kafin rattafa hannun, an ruwaito karamar Ministar Kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, bayan taron Majalisar Zartarwar makon da ya gabata tana fada wa manema labarai cewa, gwamnatin tarayya ta fitar da wasu muhimman ayyukan raya kasa har guda 34, da za ta aiwatar a kasafin kudin banan. Ayyukan da aka dunkule wuri hudu da suka shafi tafiyar da gwamnati da matakan tsaro, da kuma canja akalar tsarin tattalin arzikin kasar nan zuwa mai dogaro da kai. Batutuwan su ne   samar da tartibiyar darajar musayar kudaden kasar nan da na waje a cikin wannan shekarar, da samun daidaito a kan kudin ruwa da Bankuna kan caja ana fatan ka da su rinka wuce kashi 9 cikin 100. Akwai aniyar gwamnati na ganin  kasar nan ta zama mai dogaro da kanta kan samar da tumatir a wannan shekarar da shinkafa nan da shekarar 2018.
Kazalika a kasafin kudin na bana in ji Minista Uwargida Shamsuna Ahmed, akwai kudurin yadda za a kara yawan masara da waken soyar da ake nomawa da ma kaji da dabbobi, duk da aniyar daina shigo da su a cikin kasar nan, nan da wani dan lokaci. Akwai kuma batun kammala aikin ginin layin dogo daga Kaduna zuwa Abuja zuwa Abuja a bana, baya ga gyara da gina wasu manya da kananan hanyoyi 31, sai batun gyaran Cibiyoyin kiwon lafiya dubu biyar (5,000), a wasu mazabu 5,000, na kasar nan. A gefe daya kuman kasafin kudin na bana yana kunshe da wasu makudan kudi har =N= biliyan 350 da za a saka su cikin fannonin da za su habaka tattalin arzikin kasar nan kai tsaye.
A cikin jawabinsa bayan ya rattafa hannu kan kasafin kudin, Shugaba Bahari ya sake nanata aniyar gwamnatinsa na ganin lallai daga wannan kasafin kudi `yan kasa sun fara rage radadin kuncin rayuwar da suke ciki, wanda ya tabbatar da cewa `kasar nan da `yan kasar ba su taba samun kan su a cikinta ba. Ya jaddada cewa, yana ji kuma yana sane da irin mawuyacin halin kuncin rayuwar da talakawa suke ciki da fatan za su kara hakuri
Kamar yadda Shugaba Bahari ya kira kasafin kudin na bana“Kasafin kudin Canji,” Canjin da dama shi ne taken jam`iyyarsa ta APC, kuma don neman Canjin alheri ta kowane fannin rayuwa ta sa `yan kasa suka zabi APC din suka ki PDP, a zabubbukan bara, to kuwa lallai `yan kasa sun zaku su ga wannan canji a cikin akussansu, bisa ga irin tsananin mawuyacin halin rayuwar da suke ciki, wanda gwamnatin na ta ikirarin tana sane da su.
Da wadannan muhimman bukatun `yan kasa, ya zama wajibi shugaban kasa da ministoci da sauran mukarraban gwamnatin, su tashi tsaye wajen ganin sun aiwatar da kasafin kudin na bana yadda mafi yawan `yan kasa za su gani a kasa, wai an ce da ‘kare ana biki a gidansu…’ Wannan shi ne kasafin kudin wannan gwamnatin na farko a cikin zangonta na farko mai wa`adin shekaru hudu, wanda tuni ta yi daya. Don haka shi ne zakaran gwajin dafinta na salon mulkin ceton al`umma da tak e ta ikirari zai kasance a sauran shekarun da take da su. Lallai `yan kasa sun zuba idanu da fatan kowa zai ba da tashi gudummuwar, don aikin ba na gwamnati kadai ba ne.