Kasafin kudin shekarar 2018 ya kai Triliyan 8.6

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya shiya gabatar da Naira triliyan 8.6 a matsayin kasafin kudin badi. Wannan kasafin, idan har aka tabbatar da shi, zai zama cewa an samu karin kashi 15 ke nan a kan kasafin bara, wanda aka yi na kimanin Naira triliyan 7.44. Amma dai za a iya samun sauye-sauye a kasafin […]

Kasafin kudin shekarar 2018 ya kai Triliyan 8.6
Kasafin kudin shekarar 2018 ya kai Triliyan 8.6

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya shiya gabatar da Naira triliyan 8.6 a matsayin kasafin kudin badi.

Wannan kasafin, idan har aka tabbatar da shi, zai zama cewa an samu karin kashi 15 ke nan a kan kasafin bara, wanda aka yi na kimanin Naira triliyan 7.44.

Amma dai za a iya samun sauye-sauye a kasafin kudin daga shugaban qasar, ko kuma majalisa. Sannan kuma Gwamnatin Tarayya ta ce za ta gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa a watan Oktoba.

Shi dai wannan kasafin kudin, an shirya shi ne a kan zaton cewa za a riqa sayar da gangan mai a Dala 45, sannan kuma za a riqa haqo ganga miliyan 2.51 a kullum. Sannan kuma canjin Dala, a Naira 305 akan kowace Dalar Amurka.