kasar Burma na yunkurin kafa dokar hana musulunta

A shekaranjiya Laraba ne Majalisar Dokokin kasar Burma (Myanmar) ta fara zama don tattaunawa kan dokar da za ta hana mutanen kasar canja addini zuwa Musulunci da kuma hana aure a tsakanin masu bin addinai mabambanta don kare addinin Budha mafi rinjaye a kasar.Wannan yunkuri ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba […]

kasar Burma na yunkurin kafa dokar hana musulunta
kasar Burma na yunkurin kafa dokar hana musulunta

A shekaranjiya Laraba ne Majalisar Dokokin kasar Burma (Myanmar) ta fara zama don tattaunawa kan dokar da za ta hana mutanen kasar canja addini zuwa Musulunci da kuma hana aure a tsakanin masu bin addinai mabambanta don kare addinin Budha mafi rinjaye a kasar.
Wannan yunkuri ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar a kasar sakamakon barkewar rikici a tsakanin mabiya addinin Buddha da Musulmi, inda aka kashe mutum 237 da raba sama da dubu 140 da muhallinsu un daga watan Yunin shekarar 2012.
 Galibin wadanda aka kashe ko aka raba da muhalli Musulmi, wadanda suke da kashi biyar kacal cikin 100 na jama’ar kasar mai mutum miliyan 60.
A ranar Talata ce wata jaridar kasar ta buga daftarin kudirin dokar da zai bukaci duk mai son canja addininsa ya nemi wasu kwamitocin jami’an gwamnati da ke kowane gari.
kudirin dokar na daga cikin irinsa uku da gwamnatin kasar ke son gabatarwa, kuma daga cikin manufar dokar har da rage haihuwa da hana auren mace fiye da daya da kuma hana aure a tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Wani babban limamin Buddha mai suna Dhammapiya ne ya taimaka wajen rubuta ainihin kudirin dokar ya ce an tsara dokar ce domin karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai tare da ‘kare mata’ ’yan Buddha daga tilasta musu karbar Musulunci a lokacin da suke auren Musulmi.
Sai dai wata mai kare hakkin mata mai suna May Sabe Phyu, ta yyi watsi da da’awar cewa dokar za ta kare hakkin mata. Ta ce, “Addini zabi ne na daidaikun mutane. Don haka mene ne manufar kafa dokar hana sauya addini?”
Misis May Sabe Phyu ta ce ana son kafa dokar ce da niyyar kuntata wa Musulmi, “An kafa ta ce domin tsananin kiyayya, kuma ta mayar da hankali ne kan wani addini guda,” inji ta.
Misis May Sabe Phyu wadda iyayenta mabiya addinin Buddha da Kirista ne ta ce babu kungiyar mata ko ta addini baya ga na Buddha da aka tuntuba yayin tsara kudirin dokar.
 “An yi komai a boye,” inji ta inda ta ce, kamata ya yi ’yan majalisar su fi mayar da hankali kan kafa dokokin game da cin zarafin mata, wanda bai tsaya a tsakanin mabiya addini daya a akasar ba.