kasar China ta tilasta Musulmi su rika sayar da giya da taba don ‘raunana’ Musulunci
Mahukuntan kasar China sun umarci Musulmi masu shaguna da gidajen sayar da abinci a wani kauye da ke yankin dinjiang da ke fama da rikici kan su rika sayar da giya da taba tare da tallata su “karara” a wani yunkuri na raunana Musulunci a idon mutanen yankin. Gidan rediyon Radio Free Asia (RFA) wanda […]
Mahukuntan kasar China sun umarci Musulmi masu shaguna da gidajen sayar da abinci a wani kauye da ke yankin dinjiang da ke fama da rikici kan su rika sayar da giya da taba tare da tallata su “karara” a wani yunkuri na raunana Musulunci a idon mutanen yankin.
Gidan rediyon Radio Free Asia (RFA) wanda ya ruwaito labarin ya ce ana barazana ga shaguna da gidajen abincin da suka gaza bin wannan umarni cewa za a rufe tare da hukunta masu su.
kasar China ta kaddamar da ‘miyagun’ kamfe na raunana riko da addinin Musulunci a yankin dinjiang mai yawan Musulmi da ke yammacin kasar.
An hana wa ma’aikatan gwamnati da yara ’yan makaranta yin azumin wata Ramadan a bara, sannan a wurare da dama an hana mata sanya nikabi yayin da ake hana maza ajiye dogon gemu.
A kauyen Aktash da ke kudancin dinjiang, wani jigo a Jam’iyyar Communist Party mai suna Adil Sulayman, ya shaida wa gidan rediyon RFA cewa masu shaguna da dama sun daina sayar da giya da taba tun shekarar 2012 “saboda tsoron fushin jama’a’ yayin da wasu mutanen kauyen suka yanke shawarar kaurace wa shan giya ko zukar taba.
Ya ce Alkur’ani ya bayyana kayan maye da laifi ne, yayin da wasu malaman Musulunci suka hana shan taba.
Sulayman ya ce mahukunta a birnin dinjiang suna ganin ’yan kabilar Uighurs da ba su shan taba da masu tsananin kishin addini, don haka ne suka kafa dokar hana yaduwar biyayya ga addinin wanda hakan kuma ke barazana ga zaman lafiya.
“Muna kamfe ne don raunana addini a nan, kuma wannan bangare ne na kamfe din,” ya shaida wa wata kafar labarai da ke Washington.
Wata sanarwa da RFA ya samu wadda kuma aka watsa ta kafar sadarwar Twitter, ta umarci dukkan masu gidajen abinci da shaguna da ke Aktash su sayar da akalla nau’i biyar na giya da taba kuma su rika baje su a filin da kowa zai gani. “Duk wanda ya ki bin wannan umarni za a rufe shagonsa a dakatar da kasuwancinsa kuma a dauki matakin shari’a a kansa,” inji sanarwar.
China ta ce mayakan Uighur da ke zaune a kasashen waje na amfani da Intanet wajen karafa gwiwar Musulmin yankin su kaddamar da jihadi kan kasar. Sai dai kuma manazarta sun ce dogon lokacin da kasar China ta dauka tana danniya da musguna wa Musulmin Uighur ne ya sa jama’ar komawa ga Musulunci a matsayin hanyar da za ta kare musu ’yanci, kuma hakan ne ya jefa kadan daga cikinsu ga tayar da kayar baya. Sun yi gargadin cewa tilasta Musulmi sayar da giya da taba da haramta sanye dan kwali da ajiye gemu ba za su haifar da da mai ido ba.
Sulayman ya ce kimanin shaguna da dakunan sayar da abinci 60 ne a yankin suka bi wannan umarni na gwamnati.