Kasar Ghana ta cire tallafin man fetur
Kasar ta ce daukar matakin ya zama wajibi a halin yanzu
Kamfanin Mai na Kasar Ghana (NPA) ya sanar da cire tallafin mai gaba daya a kasar.
Daukar matakin dai na daya daga cikin irin sauye-sauyen da kasar ke aiwatarwa don tabbatar da daidaita bangaren albarkatun man fetur na kasar.
- Malamin Islamiyya ya yi wa dalibansa 4 ’yan gida daya fyade a Bauchi
- Motar siminti ta muttsuke mutum 3 har lahira
Shugaban kamfanin, Abdul Hamid, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron makon matatun mai da masu rarraba shi na nahiyar Afirka na shekarar 2023 da yake gudana yanzu haka a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.
Ya ce gwamnatin kasar, ta hannun kamfanin na NPA ta cire tallafin na dukkan makamashin kasar.
Ya ce, “Mun cire tallafinmu, kuma mun mayar da harkokin gaba daya ga kasuwanni. Daukar matakin ya zama wajibi saboda gwamnati na shan matukar wahala wajen biyan kudaden tallafin.
“Amma duk da haka, za mu tabbatar masu sayen man ba su fada halin ni-’ya-su ba saboda cire tallafin,” in ji Abdul Hamid, lokacin da yake jawabi a kan manufofin da kamfanin ya aiwatar.
Ya ce sun cire tallafin ne saboda daidaita halin rashin tabbas din da kasuwa man fetur da ta iskar gas ta kasar suka fada sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.
“A karon farko cikin shekara 30, mun sanya iyakar abin da za a iya biya na farashin mai da ma so ya wuce haka domin daidaita yanayin kasuwar,” in ji shi.
Shugaban kamfanin ya kuma ce sun kirkiri wani asusu na musamman da zai taimaka wa matatun mai su kara adadin man da suke tacewa da ganga 50 a kullum domin samar da wadataccen man da zai ishi kasar.