‘kasar Holland na da hannu a kisan Musulmin Bosniya’
A shekaranjiya ne wata kotun kasar Holland ta dora wa gwamnatin kasar alhakin mutuwar Musulmi fiye da 300 a Srebrenica lokacin yakin Bosniya- Hercegobina da aka yi a watan Yulin shekarar 1995.Musulmin dai yawanci yara ne da mata da suke gudun-hijira a wani sansanin Majalisar dinkin Duniya, amma sai dakarun rundunar wanzar da zaman lafiyar […]
A shekaranjiya ne wata kotun kasar Holland ta dora wa gwamnatin kasar alhakin mutuwar Musulmi fiye da 300 a Srebrenica lokacin yakin Bosniya- Hercegobina da aka yi a watan Yulin shekarar 1995.
Musulmin dai yawanci yara ne da mata da suke gudun-hijira a wani sansanin Majalisar dinkin Duniya, amma sai dakarun rundunar wanzar da zaman lafiyar kasar Holland suka mika su ga sojojin Sabiyawa, wadanda su kuma sukai masu kisan gilla.
Alkalin kotun da ke birnin Hague ta ce ta gamsu da hujjojin da suka tabbatar da cewa da an kyale mutanen sun ci gaba da zama a sansanin da wata kila ba su gamu da ajalinsu ba.
Wata kungiyar mata da ke kare Hakkin Bil’adama ta Mothers of Srebrenica ce ta shigar da kara a gaban kotun, tana zargin gwamnatin kasar da gazawa wajen kare dubban jama’ar da ke sansanin Majalisar dinkin Duniya.
Wannan ne dai mummunar tashin hankalin da ya faru a nahiyar Turai tun bayan Yakin Duniya na biyu. Kuma yakin ya yi sanadiyyar mutuwar Musulmi kusan su dubu 8.