kasar Hungary ta fara tantance ‘yan gudun hijira
A shekaran jiya Laraba kasar Hungary ta fara shirin gaggauta duba takardun neman mafaka da masu kaura za su gabatar a hanyoyin shiga kasar ta kudanci.Hukumomin kasar sun ki amincewa da rukunin farko na masu neman mafaka wadanda suka fito daga Bangladesh, saboda sai da mutanen suka wuce ta Serbia, wadda Hungarin take gani nan […]
A shekaran jiya Laraba kasar Hungary ta fara shirin gaggauta duba takardun neman mafaka da masu kaura za su gabatar a hanyoyin shiga kasar ta kudanci.
Hukumomin kasar sun ki amincewa da rukunin farko na masu neman mafaka wadanda suka fito daga Bangladesh, saboda sai da mutanen suka wuce ta Serbia, wadda Hungarin take gani nan ma mafaka ce ga masu kaurar.
Masu kaura da yawa ne suka shafe daren ranar Talata a bakin iyakar kasar Serbia da Hungary, bayan hukumomi a Hungarin sun rufe hanyoyin shiga kasar.
‘Yan sandan kasar sun ce ‘yan gudun hijira fiye da 400 ne suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba ranar Talata.
A cikin watan jiya kawai, fiye da ’yan gudun hijira dubu 156 ne suka shiga nahiyar Turai. Jimullah fiye da rabin miliyan ne suka shiga nahiyar daga farkon bana zuwa yanzu. Galibin ‘yan gudun hijiran dai sun fito ne daga kasashen Siriya da Iraki saboda rikicin da kasashen ke ciki.