kasar Taiwan ta tallafa wa ’yan gudun hijirar Najeriya da kekunan guragu 200

Gwamnatin kasar Taiwan ta ba wa ’yan gudun hijira tallafin kekunan guragu 200, inda Jakadan kasar Taiwan a Najeriya, Mista Morgan Chao jim kadan ya mika tallafin ga Shugaban kungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya, a hedikwatarta da ke Abuja.A jawabin Jakada Morgan Chao ya ce gwamnatin Taiwan ta dauki matakin ne don tallafa […]

kasar Taiwan ta tallafa wa ’yan gudun hijirar Najeriya da kekunan guragu 200
kasar Taiwan ta tallafa wa ’yan gudun hijirar Najeriya da kekunan guragu 200

Gwamnatin kasar Taiwan ta ba wa ’yan gudun hijira tallafin kekunan guragu 200, inda Jakadan kasar Taiwan a Najeriya, Mista Morgan Chao jim kadan ya mika tallafin ga Shugaban kungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya, a hedikwatarta da ke Abuja.
A jawabin Jakada Morgan Chao ya ce gwamnatin Taiwan ta dauki matakin ne don tallafa wa kokarin kungiyar Red Cross wajen kula da wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa a kasar nan. “Ina farin cikin mika wannan tallafi da ke da manufar taimakawa wajen rage wahalhalu da wasu ’yan uwanmu nakasassu da ke gudun hijira suka shiga sakamakon ayyukan ta’addanci na Boko Haram da makamantanta. Ina fata kungiyar za ta yi adalci wajen raba wadannan sababbin kekunan guragu 200 da muka bayar,” inji shi.
Da yake mayar da jawabi Shugaban kungiyar Red Cross Society ta kasa, Mista Bolaji Anan Akpan ya jinjina wa gwamnatin Taiwan kan tallafin wanda a cewarsa ba shakka zai taimaka wajen rage wa ’yan gudun hijirar musamman nakasassu cikinsu wahalhalu. Ya yi fatar dorewar kyakkyawan dangantakar da ke tsakanin kungiyarsa da ofishin Jakadan Taiwan a Najeriya inda ya ce za a yi adalci wajen rabon kekunan.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe