Kasar Zimbabwe na cikin rudani

Har zuwa ranar Alhamis da safe, kasar Zimbabwe na cikin rudani da rashin tabbas kan makomar siyasar kasar da kuma makomar Shugaban kasar Robert Mugabe domin sojin kasar na ci gaba da rike ikon gudanar da kasar.  BBC ta ruwaito cewa ana ci gaba gudanar da tattaunawa a kasar da kuma a Botswana mai makwabtaka […]

Kasar Zimbabwe na cikin rudani

Har zuwa ranar Alhamis da safe, kasar Zimbabwe na cikin rudani da rashin tabbas kan makomar siyasar kasar da kuma makomar Shugaban kasar Robert Mugabe domin sojin kasar na ci gaba da rike ikon gudanar da kasar. 

BBC ta ruwaito cewa ana ci gaba gudanar da tattaunawa a kasar da kuma a Botswana mai makwabtaka kan makomarta.

“Wakiliyar BBC ta ce ko da yake, Mista Mugabe ya kubuce wa takunkuman kassarawa da kasashen Yamma suka kakaba da kuma matsin lamba daga ‘yan adawa da ke da karfi a baya. Amma sai ga shi makusantansa sun tade shi ya fadi.” 

Hakanan kuma BBC ta ruwaito wani jagoran adawan kasar mai suna Tendai Biti, inda ya bukaci sojoji su mayar da kasar kan mulkin dimokradiyya ta hanyar kafa wata hukumar wucin gadi da za ta yi jagora zuwa zabe.

Ita dai rundunar sojin kasar tana ci gaba da nanata cewa ba Shugaba Mugabe suke nema ba, domin a cewarsu, shugaban da iyalansa suna cikin koshin lafiya, amma dai sun nuna cewa suna neman wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa ne.

Ya zuwa lokacin hada wannan labarin, an kama Ministan Kudin kasar, Ignatius Chombo, da kuma shugaban matasan Jam’iyyar ZANU-PF mai mulki.

Sannan kuma kafar yada labarai ta Yahoo, ta ruwaito cewa akwai rade-radin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar da aka tsige Emmerson Mnangagwa, shi ne ya shirya wannan “juyin mulkin”. Don haka ba za a yi mamaki ba idan har ya zama shugaban kasar.

Tsige tsohon mataimakin shugaban kasar da Shugaba Mugabe ya yi domin ya ba matarsa Grace dama ta zama mataimakiyarsa ne ya janyo wannan dambarwar da ake ciki.