Kasashe 130 sun amince da ’yancin kasar Palasdinu
Ranar 28 ga watan nan na Mayu, 2024, kasashen Spain, Norway da Ireland za su fara hulda da Palasdinu a matsayin kasa mai cikakken ’yanci
Kungiyar fafutikar ’yancin Palasdinawa (PLO) ta sanar cewa, kasashe 130 daga cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 sun amince da ba wa kasar Palasdinu cikakken ’yanci, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta ruwaito.
Kazalika, manyan kasashen Turai uku, Spain, Norway da Ireland sun janye jakadunsu daga kasar Isra’ila kan yakin da take da kuma kashe Palasdinawa a Zirin Gaza.
Firaministan Ireland, Harris Simon, shaida wa taron manema labarai a birnin Dublin a ranar Laraba, cewa kasashe ukun sun yi itifakin mu’amala da Palasdinu a matsayin kasa mai cikakken ’yanci.
Ministan harokin wajen Ireland, Micheál Martin, ya ce daukar Palasdina a matsayin mai cikakken iko da za su yi zai fara aiki ne daga ranar 28 ga watan nan na Mayu, 2024.
Wannan mataki wani gagarumin kokari na kara kaimi ga yunkurin samun yancin Palasdinawa da kuma juya baya ga Isra’ila.
Firaminstan Norway, Jonas Gahr Støre, ya ce yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, “ya nuna karara cewa zaman lafiya da aminci ba zai samu ba, har sai an yi wa Palasdinawa adalci.
“A wannan yanayi da aka kashe rayuka sama da rayuka 35,000 dole ne a nemo mafita ga rikicin Isra’ila da Palasdinawa: Inda kowannensu zai kasance kasa mai cikakken ’yanci.”
“Mun yi haka ne domin a samu zaman lafiya da juna, amma ba wai don muna kyamar Isra’ila ko yahudawa ba, ko kuma don mu fifita Palasinawa da Hamas.”
Sai dai Isra’ila ta soki matakin kasahen, inda Ministan Harkokin Wajenta, Israel Katz, ya fitar da sanarwar cewa kasar “ba za ta raga wa duk wadnda ke kafar ungulu ga ’yancinta da kuma tsaronta ba.