Kasashe 23 da suka sanya wa jiragen Rasha takunkumi

Rasha ta dauki matakin ramuwar gayya kan kasashen da suka sanya wa jiragenta takunkumi

Kasashe 23 da suka sanya wa jiragen Rasha takunkumi

Jirgin Rasha.

Rasha ta yi ramuwar gayya a kan wasu kasashen Turai akalla takwas inda ta sanya musu takunkumi bayan sun haramta wa jiragensu sauka ko bi ta cikin kasashensu.

Kasashe akalla 22 daga Kudancin da Arewacin nahiyar Turai sun haramta wa jiragen Rasha bi ta sararin samamiyarsu, ballantana yada zango ko sauka a filayen jirginsu a wani mataki na nuna adawarsu ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine da yaki.

Ba su kadai ba, hatta Kanada, wadda ba a nahiyar take ba, ita ma ta dauki irin wannan mataki, bayan dakarun Rasha sun auka wa Ukraine da yaki.

Ga jerin kasashen da suka haramta wa jiragen Rasha amfani da sararin samaniyarsu ko sauka ko yada zango a kasarsu.

Sahun farko

A ranar Juma’a Birtaniya ta zama kasa ta farko da ta haramta wa jiragen sama na kashi-kai na Rasha bi ta sararin samaniyarta.

Birtaniya ya yi hakan ne bayan a ranar Alhamis dakarun Rasha sun far wa Ukraine da yaki, bisa umarnin Shugaba Vladimir Putin.

A ranar Juma’ar gwamnatocin Poland, Bulgariya da Jamhuriyar Czech suka ce daga karfe 12 na dare sun haramta wa jiragen Rasha shiga kasashensu.

Zuwa ranar Asabar, kasashen Estonia, Latvia, Lithuania, Slovenia da Romania suka bi sahu.

Fira Ministan Estonia, Kaja Kallas, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Jiragen masu nuna fin karfi ba su da wuri a sararin samaniyar masu kare dimokuradiyya.”

Jamus da Austria

A ranar Lahadi ce gwamnatin Austria ta sanar cewa daga karfe 2 na rana ta haramta wa duk wani jirgin Rasha amfani da filin jirgi ko sararin samaniyar kasarta.

A wani sako da shugaban kasar, Karl Nehammer, ya wallafa a Twitter, ya ce, “Muna yin duka abin da ya kamata na nuwa a Vladimir Putin cewa ba ma goyon bayan mamayarsa a Ukraine.”

Jamus kuma ta kakaba wa jiragen Rasha takunkumin shiga kasarta na tsawon wata uku daga karfe 2 na ranar Lahadin, amma ta ce banda jiragen ayyukan jinkai.

Faransa

Faransa ta sanar da shirinta na rufe iyaykokinta ga daukcincin jiragen Rasha daga ranar Lahadi, domin nuna adawarta ga harin Rasha a kan Ukraine.

Belgium

Ita ma kasar Belgium ta bi sahu, bayan Fira Minista Alexander De Croo ya sanar cewa, “Sararin samaniyarmu na bude ga masu sada tsakanin al’umma, amma ba masu nuna fin karfi da danniya ba.”

Kashen Nordic

Kasashen Finland, Sweden, Denmark, Norway da Iceland su ma sun sanar cewa za su haramta wa jiragen Rasha bi ta kasashensu.

Fira Ministan kasar Finland, wadda iyakarta da Rasha ke da tsawon kilimita 1,300, Timo Harakka, ya sanar a Twitter cewa kasarsa, tana “shirin rufe sararin samaniyata ga Rasha,” amma bai ba da lokaci ba.

Italiya, Spain da Malta

Su ma Italiya da Spain, suka ce sun rufe sararin samaniyarsu ga jiragen Rasha.

A nata bangaren, kasar Malta ta ce ita ma ta bi sahu, domin nuna “cikakken goyon baya ga Ukraine”.

Arewacin Macedonia

Gwamnatin Arewacin Macedonia ma ta haramta wa jiragen Rasha bi ta kasarta, amma banda jiragen ayyukan jinkai.

Kanada

Bayan haka, Kanada, wadda ba a yankin Turai take ba, ta rufe iyakokinta ga daukacin kamfanonin jiragen Rasha nan take.

A ranar Lahadi, Ministan Sufurin Kanada, Omar Alghabra, ya bayyana a cikin wani sako da ya sanya a Twitter cewa, “Za mu kama Rasha da laifin harin da ta kai wa Ukraine.”

Ramuwar gayyar Rasha

A wani mataki na ramuwar gayya, a ranar Lahadi gwamnatin Rasha ta haramta shiga kasarta ga jiragen kasashen Estonia, Latvia, Lithuania da kuma Slovenia.

Kafin nan, a ranar Asabar ta haramta wa jirage daga kasashen Bulgaria, Poland da Jamhuriyar Czech shgia kasarta.

Ko a ranar Juma’a sai da ta yi ramuwar gayya a kan kasar Birtaniya, inda ta haramta wa duk jirage masu alaka da Birtaniya shigowa kasarta.