Kasashe 25 ne za su baje kolinsu a Kasuwar Duniya ta Kano – KACCIMA
Kimanin kasashe 25 ne za su baje kolinsu a bikin baje koli na kasa da ake yi a yanzu haka a Jihar Kano. Mataimakin Shugaban Cibiyar Bunkasa Ciniki da Masana’antu da Ma’adinai da Ayyukan Gona (KACCIMA) ta Jihar Kano Ambasada Usman Darma ne ya bayyana haka a lokacin bude baje kolin a dandalin baje koli […]
Kimanin kasashe 25 ne za su baje kolinsu a bikin baje koli na kasa da ake yi a yanzu haka a Jihar Kano. Mataimakin Shugaban Cibiyar Bunkasa Ciniki da Masana’antu da Ma’adinai da Ayyukan Gona (KACCIMA) ta Jihar Kano Ambasada Usman Darma ne ya bayyana haka a lokacin bude baje kolin a dandalin baje koli da ke kan titin gidan Zoo a Kano.
Baje kolin na bana wanda aka yi masa take da “Saukaka hanyoyin kasuwanci shi ne ci gaban Najeriya da habaka kasuwancinta” shi ne karo na 39 da fara yin bajekoli a jihar.
Ambasada Usman Darma ya bayyana cewa zuwa yanzu akwai kimanin kamfanoni sama da 500 da suka hada da na gida da kuma na kasashen ketare wadanda suka zo don kulla harkar kasuwanci da jihar. “Muna sa rai bana zai fi na sauran shekaru armashi, domin daga ganin yadda abubuwa ke tafiya za a fahimci cewa za ta fi wacce aka yi a baya kasancewar kamfanoni masu yawa daga kasashen waje irin su China da Indiya da Amurka da Ingila da sauransu za su kasance a filin. Kasancewar Kano ita ce cibiyar kasuwanci a Najeriya da ma a cikin kasashen Afrika,” inji shi.
Ambasada Darma ya kara da cewa, “jami’an Hukumar Yi WA Kamfanoni Rajista CAC a take za su yi wa kamfaninka rajista ga kuma samun saukin kaso hamsin. Ina ganin wannan dama ce da bai kamata mutane su bar ta ba.”
Har ila yau Mataimakin Shugaban cibiyar ya bayyana cewa hukumomin Gwamnatin Tarayya za su kasance a wannan wuri don saukaka wa al’umma kan lamurran da suka shafe su kai tsaye “Jami’an Babban Bankin Najeriya CBN suna wurin don wayar wa al’umma kai kan wasu shirye -shiryensu na yadda al’umma za su fahimta har kuma su ci gajiyar shirye-shiryen. Haka Hukumar Sadarwa ta NCC za ta taimaka wajen share wa al’umma hawaye game da matsalolin da suke fuskanta wajen yin amfani da wayoyin hannu.”
Ambasada Darma ya ce wani karin armashi shi ne an samar da dan karamin waje wasannin yara don saukaka wa iyaye mata wajen samun sakewar duba kayayyakin da suke bukata.